Shugaban matasa na jam'iyyu biyu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a jihar Anambra

Shugaban matasa na jam'iyyu biyu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a jihar Anambra

  • Ana gab da fita filin fafatawa a zaɓen gwamnan jihar Anambra, jam'iyyar PDP ta yi wani babban kamu a wasu yankunan jihar
  • Shugabannin matasan jam'iyyu biyu tare da dubbannin masoya sun sauya sheka zuwa babbar jam'iyyar hamayya PDP a Njikoka
  • Wannan dai ya zo ne mako ɗaya kafin zaɓen gwamnan jihar, kuma kwana daya da kammala gangamin PDP na ƙasa

Anambra - Mako ɗaya kafin zaben gwamnan Anambra, shugabannin matasa na jam'iyyun AFGA da YPP, a karamar hukumar Njikoka, sun koma PDP.

Dailytrust tace shugabannin matasan sun sauya sheƙa zuwa PDP ne tare da dubbannin magoya bayan su.

Sun bayyana matakin komawa PDP ne a wurin taron yaƙin neman zaɓen PDP a ƙaramar hukumar Njikoka, da ya gudana a makarantar Igweubuike.

Kara karanta wannan

Cikin hotuna: Matashi mai shekaru 25 da ya lashe kujerar shugaban matasan PDP

Jam'iyyar PDp
Shugaban matasa na jam'iyyu biyu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a jihar Anambra Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban matasan APGA a Njikoka, Chike Uzuegbunam, da kuma shugaban jam'iyyar YPP a Njikoka, Anthony Okafor, sune suka jagoranci dubbannin mambobinsu zuwa PDP

Meyasa suka koma PDP?

A cewar Uzuegbunam, wanda ya jagoranci dubbannin mambobin APGA, sun ɗauki wannan matakin ne saboda kyakkyawan kudirin PDP da jawo kowa a jiki.

Ya kara da cewa hakan ne ya jawo hankalin su, da kuma maida hankalin ɗan takarar gwamna karkashin PDP wajen ɗaga jihar Anambra.

Hakanan kuma, Okafor, ya jagoranci dubbannin mambobin YPP zuwa jam'iyyar PDP daga dukkan sassan ƙaramar hukumar Njikoka.

Me ɗan takarar PDP yace a wurin taron?

A jawabinsa na wurin taron, ɗan takarar PDP, Ozigbo, yace:

"Wannan zaɓen dake tafe wata babbar dama ce ga al'ummar jihar Anambra su canza labarin, domin kawo canji da kyakkyawan shugabanci."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar ZLP ta ruguje yayin da shugabanta da mambobi suka koma PDP

"Mun bayyana cewa zamu fi baiwa ɓangaren tsaro fifiko domin babu wani kasuwanci da zai cigaba a muhallin da babu tsaro."
"Mai girma Peter Obi ya yi namijin kokari wajen gina tsarin tsaro, kuma zamu yi koyi daga basirarsa idan muka kai ga madafun iko."

A wani labarin kuma mun kawo muku babban dalilin da ya hana tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan halartan gangamin PDP

Jonathan ya bar Najeriya ranar Asabar domin halartar taron ƙungiyar Nahiyar Africa a Nairobi, Kenya, wanda za'a tattauna kan zaman lafiya a Africa.

Amma wasu ƙusoshin PDP na ganin tsohon shugaban ya yi amfani da wannan uzurin ne domin tsallake babban gangamin PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262