Gombe: Idan ba za ka iya ba toh ka sauka – Dankwambo ya caccaki Inuwa Yahaya

Gombe: Idan ba za ka iya ba toh ka sauka – Dankwambo ya caccaki Inuwa Yahaya

  • Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya yi hannunka mai sanda ga magajinsa, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya
  • Dankwambo ya kalubalanci gwamnan na Gombe da ya sauka idan har ba zai iya tunkarar matsalolin da ke gabansa ba a matsayinsa na jagora a jihar
  • Ya ce kokawa kan matsaloli na nuna gazawar shugaba domin shi ya kawo kansa yace zai iya

Jihar Gombe - Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya bukaci magajinsa, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, da ya tunkari matsalolin da ke gabansa maimakon kokawa a kansu.

A wani wallafa da yayi a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, Dankwambo ya ce idan Yahaya bai shirya ba, toh ya sauka daga kujerar shugabanci domin ba mutanen da za su iya damar fuskantar matsalolin.

Kara karanta wannan

Na'Abba: Buhari ya gaza shawo kan matsalolin Najeriya ne saboda ba ya neman shawara

Gombe: Idan ba za ka iya ba toh ka sauka – Dankwambo ya caccaki Inuwa Yahaya
Gombe: Idan ba za ka iya ba toh ka sauka – Dankwambo ya caccaki Inuwa Yahaya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya ce kokawa game da matsalolin na nuna gazawarsa a matsayinsa na jagora.

Dankwambo ya ce duk mutumin da ke gabatar da kansa a matsayin shugaba toh ya zama wajibi ya shirya ma kalubale.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“A lokacina, ban taba kukan cewa babu kudi da zan gudanar da gwamnatina ba, saboda ni na gabatar da kaina cewa ina so na zama gwamna.
“Daga ranar da shugaba ya fara kukan cewa akwai abu kasa, akwai wannan, hakan na nufin akwai gazawa a shugabancinsa.
“Don haka, idan baka shirya fuskantar matsaloli ba a matsayin shugaba toh sai ka sauka ka ba wadanda suka shirya tunkarar matsaloli dama.”

Gwamnatin Gombe Ta Kashe N100m a 2021 Kan Kiristoci Mahajjata, Jami'ai

A wani labari na daban, Karu Ishaya, sakataren hukumar samar wa da mahajjatan addinin kirista walwala, CPWB, na jihar Gombe ya bayyana yadda gwamnatin jihar Gombe ta kashe fiye da naira miliyan 100 wurin daukar nauyin mahajjatan kiristoci 70 zuwa kasar Jordan.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa daga arewa maso gabas zai kawo karshen ta’addanci - Gwamna Fintiri

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Ishaya ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Otal din Dead Sea Spa dake Sweimeh a Jordan yayin amsa tambayoyin manema labarai.

A cewarsa irin karamcin da gwamnatin jihar ta nunawa masu bautar ya sa su matukar farin ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng