Gwamnatin Gombe Ta Kashe N100m a 2021 Kan Kiristoci Mahajjata, Jami'ai

Gwamnatin Gombe Ta Kashe N100m a 2021 Kan Kiristoci Mahajjata, Jami'ai

  • Karu Ishaya, sakataren hukumar walwalar mahajjata kiristoci na jihar Gombe, ya ce gwamnatin jihar ta kashe fiye da naira miliyan 100 wurin tallafawa mahajjata
  • Ishaya ya bayyana hakan ne a otal din Dead Sea Spa dake Sweimeh dake Jordan yayin amsa tambayoyin manema labarai
  • A cewarsa, cikin kudaden da gwamnati ta narka har da kudaden da aka yi amfani dasu wurin yi wa mahajjatan guda 70 gwajin cutar COVID-19

Gombe - Karu Ishaya, sakataren hukumar samar wa da mahajjatan addinin kirista walwala, CPWB, na jihar Gombe ya bayyana yadda gwamnatin jihar Gombe ta kashe fiye da naira miliyan 100 wurin daukar nauyin mahajjatan kiristoci 70 zuwa kasar Jordan.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Ishaya ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Otal din Dead Sea Spa dake Sweimeh a Jordan yayin amsa tambayoyin manema labarai.

Kara karanta wannan

Zargin karkatar da dukiyar kasa: Gwamnonin jihohi 36 sun maka Buhari a kotu

Gwamnatin Gombe Ta Kashe N100m a 2021 Kan Kiristoci Mahajjata, Jami'ai
Gwamnatin Gombe Ta Kashe N100m a 2021 Kan Kiristoci Mahajjata, Jami'ai. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Facebook

Gwamnati ta tallafawa mahajjata

A cewarsa irin karamcin da gwamnatin jihar ta nunawa masu bautar ya sa su matukar farin ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa an yi amfani da wani bangare na kudin wurin yi wa mahajjatan gwajin cutar COVID-19, Daily Nigerian ta wallafa.

Ya ce gwamnatin jihar tayi duk wani kokari na ganin ta biya kudin gwajin cutar COVID-19 ga mahajjatan har da wadanda suka biya wa kansu hajjin.

Gwamnatin jihar tana nuna kwadayinta kwarai akan harkokin addinai. Game da kokarin da gwamnatin jihar Gombe tayi, ina bukatar mutane su mika godiyarsu gare ta duk da halin tsananin rayuwar da ake ciki a halin yanzu.
Idan aka duba yadda gwamnatin jihar Gombe ta kashe fiye da naira miliyan 100 duk don taimakawa addinin Allah, dole a godewa gwamna Inuwa Yahaya bisa yi mana hidimar akan abinda ya kawomu Jordan, a cewar Ishaya.

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

Hajji yana karawa jama'a Imani

A cewarsa, hajji yana kara wa mabiya addini imani musamman kaje ka hani kuma ka koma ka cigaba da aiwatar da abubuwan da ka gani ta hanyar yin wa’azi da ya da soyayya.

Ya bukaci mahajjatan da su dauki damarar samar da hadin kai idan sun koma gidajensu.

A matsayinmu na kiristoci a jihar Gombe, ya kamata mu cire kabilanci mu rungumi kowa a matsayin ‘yan uwan da babu wanda ya isa ya raba mu.

Dangane da cutar COVID-19, Ishaya ya ce babu wani abin fargaba don yanzu haka mutum daya kacal aka samu da cutar kuma yanzu haka an killace shi ana kulawa da lafiyarsa.

A cewarsa, an gwada duk sauran mahajjatan har sau biyu kumu duk babu wanda yake dauke da cutar.

An tsinci gawar ɗan sanda, matarsa da ƴaƴansu 5 a cikin gidansu

Wani abin bakin ciki ya faru a kauyen Elegbaata, Oke Suna, Apomu, karamar hukumar Isokan a jihar Osun bayan an tsinci gawar mutum bakwai - miji, mata da yaransu biyar - a cikin gidansu, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Muna kashe N8m kulli yaumin wajen ciyar da dalibai a jihar Enugu, Minista Sadiya

Sahara Reporters ta ruwaito cewa an ceto mutum daya daga iyalansu wanda shima ya kwana a gidan an garzaya da shi asibiti a Apomu, inda ake ba shi kulawa.

Wani mazaunin garin, da ya nemi a sakayya sunansa, ya ce mutum takwas ne suka kwana a gidan a ranar Litinin, amma an tsinci gawar bakwai da safen ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel