Na kammala shirin karbar mulkin Najeriya daga hannun shugaba Buhari a 2023, Gwamna

Na kammala shirin karbar mulkin Najeriya daga hannun shugaba Buhari a 2023, Gwamna

  • Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, yace a shirye yake ya amsa kiran yan Najeriya na fitowa takarar shugaban ƙasa a 2023
  • Gwamnan yace nasarorin da ya samu a jihar Kogi, sune suka jawo hankalin yan Najeriya, har suke bukatar ya shugabanci ƙasa
  • A cewarsa duk da lokacin bai kammala wa'adin mulkinsa na biyu ba, amma muradin ƙasa ya wuce na Kogi

Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa a shirye yake ya cigaba da jagorancin Najeriya bayan shugaba Buhari ya ƙare wa'adinsa a 2023, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Da yake jawabi a cikin shirin Arise TV ranar Litinin, Gwamna Bello yace nasarorin da ya samu a Kogi su ake bukata a matakin ƙasa.

Ya kuma ƙara da cewa kyakkyawan mulkin da ya yi wa mutanen Kogi a shekaru 6 da suka wuce ne yasa mutane daga sassa daban-daban suke kiran ya nemi takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Mutum hudu sun mutu yayin da rikici ya barke tsakanin mutanen gari da fulani makiyaya a Kaduna

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi
Na kammala shirin karbar mulkin Najeriya daga hannun shugaba Buhari a 2023, Gwamna Hoto: herald.ng
Asali: UGC

Meyasa yan Najeriya ke son Gwamna Yahaya?

Wani sashin jawabinsa yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Shekara 6 kenan muna kan mulki, an samu haɗin kai a Kogi fiye da kowane lokaci. Daga nan zuwa 2023 abubuwan da muka cimma a Kogi su ake bukata a matakin ƙasa."
"Idan yan Najeriya daga kowane ɓangare, suna bibiyar jagorancin mu a Kogi, haɗa kan jama'a, neman shawarin masana, kyakkyawan shugabanci, baiwa kowa haƙƙinsa, wanda shi ake bukata a matakin kasa."
"Idan har waɗannan abubuwan yan Najeriya suka hanga suke neman na gaji shugaban ƙasa Buhari a 2023, to na amince kuma a shirye nake."

Meyasa ba zai bari ya ƙarasa mulkinsa a Kogi ba?

Da aka tambayeshi meyasa ba zai bari sai bayan ya kammala zangon mulkinsa na biyu a shekarar 2024 ba, Gwmanan yace muradin yan ƙasa ya zarce na shi da kuma na mutanen Kogi.

Kara karanta wannan

Wasu gwamnonin Arewa sun bada tallafin miliyan N20m ga iyalan mutanen da aka kashe a Sokoto

"Yiwa Najeriya aiki ya zarce na mutanen Kogi, kuma da izinin Allah da zaran an rantsar da ni a matsayin shugaban ƙasa bayan Buhari, yan Najeriya zasu samu kwanciyar hankali."

A wani labarin kuma Gwamnonin Kudu sun bukaci shahararren malami a Najeriya ya daina caccakar Shugaba Buhari

Gwamnonin yankin kudu maso gabas sun roki shahararren malamin nan na addinin kirista, Rabaran Ejike Mbaka, ya daina magana mara ɗaɗi akan shugaban ƙasa Buhari .

Shugaban gwamnonin yankin, Gwamna David Umahi, tare da rakiyar gwamna Ifeanyi Ugwuanyi, na jihar Enugu , sune suka roki malamin amadadin sauran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262