Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar Hamayya PDP ta dakatar da manyan jiga-jiganta 10
- Rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP ya ɗauki wani sabon salo a jihar Edo, inda jam'iyya ta dakatar da mambobinta 10
- Rahoto ya bayyana cewa waɗanda PDP ta dakatar magoya bayan gwamna Obaseki ne, kuma tare suka shiga PDP daga APC
- PDP ta zargi mutanen da kokarin yi wa jam'iyya zagon ƙasa, fatali da umarnin shugabannin jam'iyya da sauransu
Edo - Rikicin cikin gida a babbar jam'iyyar adawa, PDP a jihar Edo ya ɗauki sabon salo yayin da jam'iyyar a gunduma ta 2, karamar hukumar Etsako West a jihar Edo ta dakatar da mambobinta 10.
Vanguard ta rahoto cewa PDP ta ɗauki wannan matakin ne a kan mutanen saboda zarginsu da yi wa jam'iyya zagon ƙasa.
Rahotanni sun bayyana cewa mafi yawan waɗanda PDP ta dakatar sabbin mambobi ne da suka shiga PDP daga APC tare da Gwamna Obaseki da mataimakinsa Philip Shu'aibu.
Takardar dake ɗauke da matakin dakatarwan ta samu sa hannun shugaban jam'iyya na gunduma, Suileman Momodu, da sakatarensa, Elamah Abdulganinu, da wasu mutum 17.
Meyasa aka dakatar da mutanen?
A takardar, PDP ta bayyana laifukan su da yasa aka ɗauki matakin dakatar da su, wanda suka haɗa da:
"Saɓa wa dokokin mulkin jam'iyya da manufofinta, rashin ɗa'a da kuma ƙin biyayya ga umarnin jam'iyya da shugabanninta."
"Hakanan da zagon ƙasa wa jam'iyya, kokarin raba kawunan mambobin jam'iyya, da kuma kokarin hana jam'iyya gudanar da harkokinta."
Me waɗanda PDP ta dakatar suka ce?
Duk wani kokarin na jin ta bakin ɗaya daga cikin mutanen da PDP ta dakatar, Hassan Bawa, ya ci tura, domin bai amsa kiran wayar salula da aka masa ba.
Amma wani mamban PDP a gundumar, Momodu, ya bayyana cewa dakatarwan da aka musu saboda zargi ya yi dai-dai.
Jiga-Jigai da mambobin jam'iyyar APC sama da 5,000 sun sauya sheka zuwa Jam'iyyar PDP a wannan jihar
A cewarsa matakin da shugabannin jam'iyya suka ɗauka kan mutanen yana kan dokar da aka kafa PDP a kansu.
A wani labarin kuma Gwamnonin Kudu sun bukaci shahararren malami a Najeriya ya daina caccakar Shugaba Buhari
Gwamnonin yankin kudu maso gabas sun roki shahararren malamin nan na addinin kirista, Rabaran Ejike Mbaka, ya daina magana mara daɗi akan shugaban ƙasa Buhari.
Shugaban gwamnonin yankin, Gwamna David Umahi, tare da rakiyar gwamna Ifeanyi Ugwuanyi, na jihar Enugu , sune suka roki malamin amadadin sauran.
Asali: Legit.ng