Gwamna Makinde ya karyata rade-radin barin jam'iyyar PDP da tsayawa takarar shugaban kasa

Gwamna Makinde ya karyata rade-radin barin jam'iyyar PDP da tsayawa takarar shugaban kasa

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce baya shirin barin jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki
  • Hakazalika gwamnan ya karyata cewar yana niyan takarar kujerar shugaban kasa ko na mataimakin shugaban kasa a babban zaben 2023
  • Ya bayyana Atiku Abubakar, Aminu Tambuwal da Bala Mohammed a matsayin yan siyasar arewa da suka nuna ra'ayin takarar shugaban kasa a jam'iyyar adawar kasar

Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya karyata rad-radin da ake yi na cewa yana shirin barin jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Da yake magana a yayin wata hira da Channels TV a shirin Politics Today, Makinde ya bayyana cewa bashi da niyan takarar kujerar shugaban kasa ko na mataimakin shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Atiku, Tambuwal da Kauran Bauchi sun bayyana niyyar takara a zaben 2023, Gwamnan Oyo

Gwamna Makinde ya karyata rade-radin barin jam'iyyar PDP da tsayawa takarar shugaban kasa
Gwamna Makinde ya karyata rade-radin barin jam'iyyar PDP da tsayawa takarar shugaban kasa Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Ya ce:

“A’a, a’a. mutane su kan manta da yadda aka yi muka kai inda muke yanzu. A wannan jumhuriyar, an yi Shugaban kasa Obasanjo, Shugaban kasa Yar’Adua, Shugaban kasa Goodluck Jonathan, sannan a yanzu Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Dukkansu, Idan kuka duba, an kira su. Wasu masu ruwa da tsaki suka hadu sannan suka ce, ‘ku duba a wannan lokacin, ga wanda muke so muyi amfani da shi.”

A cewar Gwamna Makinde, shugaba Buhari ya sha alwashin cewa ba zai sake takarar shugaban kasa ba bayan ya sha kaye a hannun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a 2011, amma daga baya wasu masu ruwa da tsaki suka lamunce masa a 2015.

Jaridar The Cable ta kuma rahoto cewa gabannin babban zaben kasar, ya yarda cewa jam’iyyarsa na da mutanen da ya bayyana a matsayin fitattun ‘yan takara domin jagorantar kasar.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun nemi jam'iyyun siyasa su ba Tinubu tikitin shugabanci a 2023

Gwamnan ya bayyana wasu daga cikinsu a matsayin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi da sauransu.

Ya kuma bayyana cewa a yanzu PDP ta mayar da hankali ne kan yadda za ta gudanar da babban taronta na kasa cikin nasara.

Ya ce:

“Abun da ya fi muhimmanci a wannan mataki, wanda zan nemi goyon bayan mambobin PDP da kuma ‘yan Najeriya gaba daya, shine don Allah ku goya mana baya don samun nasara a babban taron kasa.

“Babu ta yadda za ku zama shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, koma gwamnoni idan baku da jam’iyya. Don haka abun da muke so da farko shine muyi abubuwa yadda ya kamata.”

PDP na bukatar mutane masu mutunci domin lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Fintiri

A gefe guda, Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ce jam’iyyar People Democratic Party (PDP) na bukatar mutane masu mutunci domin kula da harkokinta.

Kara karanta wannan

2023: Mun shirya tsaf don yin kaca-kaca da APC a Zamfara, mataimakin gwamna

A cewar Fintiri, ta hakan ne kadai babbar jam’iyyar adawar za ta iya lashe zaben shugaban kasa a 2023, jaridar The Cable ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba, a wajen taron jam’iyyar gabannin babban taronta na kasa da aka shirya yi a ranar 30 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng