Jerin wadanda suka yi nasara a zaben shugabancin jam'iyyun APC da PDP na jihohi

Jerin wadanda suka yi nasara a zaben shugabancin jam'iyyun APC da PDP na jihohi

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ta Peoples Democratic Party (PDP) duk sun gudanar da taron gangami don zaben shugabannin da zasu jagoranci harkokin su a matakin jiha a ranar Asabar, 16 ga watan Oktoba.

Yayin da APC ta zabi sabbin shugabanninta a yawancin jihohin tarayya, PDP ta gudanar da taron gangaminta a jihohi kalilan inda wa’adin shugabannin ya kare.

An gudanar da tarukan yayin da jihohi da yawa suka samar da wakilai biyu daga bangarori daban-daban.

Jerin wadanda suka yi nasara a shugabancin jam'iyyan APC da PDP na jihohi
Taron gangamin jam'iyyar APC daga jihar Legas | Hoto: Sanwo Olu
Asali: Facebook

Rahoton da jaridar The Cable ta yi yayi nuni da sabbin zababbun shugabannin da aka zaba a jihohin.

Ko da yake jihohi da yawa sun samar da shugabanni biyu, Legit.ng ta lura da rahoton ya mayar da hankali ne kawai ga wadanda suka yi nasara daga taron gangamin da shugabannin jam'iyyu na kasa suka amince da shi da kuma hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).

Kara karanta wannan

Zaben APC: Ministoci, Hadimai da manyan ‘Yan Majalisa suna cikin matsala a wasu Jihohi

Wadanda suka yi nasara daga jam'iyyar APC

  1. Stanley Okoro-Emegha (shugaban APC a jihar Ebonyi)
  2. Isa Achida (shugaban APC a jihar Sakkwato)
  3. Cornelius Ojelabi (shugaban APC a jihar Legas)
  4. Emeka Beke (shugaban APC a jihar Ribas)
  5. Dennis Otiotio (shugaban APC a jihar Bayelsa)
  6. Sunday Fagbemi (shugaban APC a jihar Kwara)
  7. Gboyega Famodun (shugaban APC a jihar Osun)
  8. Babato Misau (shugaban APC a jihar Bauchi)
  9. Alphonsus Eba (shugaban APC a jihar Kuros Riba)
  10. Ugochukwu Agballah (shugaban APC a jihar Enugu)
  11. Haliru Jikantoro (shugaban APC a jihar Njea)
  12. Nitte Amangal (shugaban APC a jihar Gombe)
  13. John Mamman (shugaban APC a jihar Nasarawa)
  14. Paul Omotoso (shugaban APC a jihar Ekiti)
  15. Ali Dalori (shugaban APC a jihar Borno)
  16. Macdonald Ebere (shugaban APC a jihar Imo)
  17. Omeni Sobotie (shugaban APC a jihar Delta)
  18. Emmanuel Jekada (shugaban APC a jihar Kaduna)
  19. Ade Adetimehim (shugaban APC a jihar Ondo)
  20. Sani Ahmed (shugaban APC jihar Katsina)

Kara karanta wannan

An samu kwamacala a zaben APC, mutum 4 suna ikirarin sun zama Shugabannin Jam’iyya

Wadanda suka yi nasara daga jam'iyyar PDP

  1. Tochukwu Okorie (shugaban jihar Ebonyi)
  2. Mohammed Babatunde (shugaban Kwara state)
  3. Dayo Ogungbenro (shugaban jihar Oyo)

Da alamu dan tsagin Aisha Buhari zai ci zaben shugabancin APC a Adamawa

A bangare guda, jerin sunayen 'yan takarar hadin kai da ake zargin uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta amince da su a matsayin 'yan takarar jam'iyyar APC na jihar Adamawa ne ya aka yanke hukuncin sun yi nasara a zaben shugabancin APC na jihar.

SaharaReporters ta rahoto cewa dukkan masu takarar da sunayensu ke cikin jerin hadin kai nan ba da jimawa ba za a bayyana su a matsayin wadanda suka yi nasara a taron gangamin jam'iyyar da aka yi a ranar Asabar.

Yayin da al'amura ke tafiya ta hanyar tsarin zabe, kuri'un da aka kada ya zuwa yanzu sun nuna cewa 'yan takarar da Uwargidan Shugaban kasa ke tallafawa sune wadanda aka zaba a taron gangamin.

Kara karanta wannan

Gwamnoni, jiga-jigan APC, PDP 7 da EFCC ke bincika kan batun Pandora Papers

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.