Da Dumi-Dumi: Mambobin Jam'iyyun Hamayya Sama da 5,000 Sun Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC
- Dubbannin mambobin jam'iyyun hamayya daban-daban sun bayyana sauya shekarsu zuwa jam'iyyar APC mai mulki
- Rahotanni sun nuna cewa mambobi sama da 5,000 ne suka koma APC a yankin karamar hukumar Ughelli, jihar Delta
- A cewarsu, sun ɗauki wannan matakin ne saboda gamsuwa da wakilcin mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Omo-Agage
Delta - Sama da mutum 5,000 daga jam'iyyun siyasa daban-daban ne suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Rahotanni sun nuna cewa mutanen sun koma APC ne a garuruwan Oviri-Ogor da Ughelli urban dake ƙaramar hukumar Ughelli ta arewa a jihar Delta.
Meyasa suka ɗauki wannan matakin?
Masu sauya shekar sun bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne bisa gamsuwa da wakilcin mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Ovie Omo-Agege.
Hakazalika, mutanen sun yaba wa Sanata Omo-Agege bisa tausayin al'umma da kuma manyan ayyukan raya ƙasa da yake ƙoƙarin yi a mazaɓar Delta ta tsakiya.
Samar da ayyuka ga matasa
Bugu da ƙari sun bayyana cewa mataimakin shugaban majalisar dattijai ya samar wa mutane da dama ayyukan yi.
Hakanan kuma sanatan ya tallafawa mutane da dama a harkokinsu na yau da kullum ta hanyar gudanar da ayyukan da ake bukata a yankin.
Sanata Stella Oduah ta koma APC a hukumance
Sanata mai wakiltar mazaɓar Anambra ta arewa a majalisar dattijai, Sanata Stella Oduah, tace, " Duk wanda yace Buhari ya watsar da Kudu-Gabas, to baiwa kan shi adalci ba haka yankinsa."
Oduah, bisa wakilcin Amaka Ononuju, ta faɗi haka ne a wurin taron sauya sheƙarta da ya gudana a sakateriyar APC dake Awka, baban birnin Anambra, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
A wani labarin.na daban kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yan Najeriya ne zasu baiwa PDP nasara a 2023
Atiku yace a halin yanzu mutane basu da wani zaɓi da ya wuce su sake amincewa da PDP a babban zaɓen 2023.
A ranar Asabar ne, PDP ta gudanar da gangamin tarukanta a matakin jihohi domin zaɓen shugabanninta.
Asali: Legit.ng