Ganduje ya mayar da martani kan yan majalisan da suka kai kararsa Abuja, Kabiru Gaya ya zame kansa
- Gwamnan jihar Kano yayi martani ga yan majalisan da sukayi masa tawaye
- Ganduje yace kawai sun gaza yiwa jama'arsu komai suna kokarin daura masa
- Daya daga cikin Sanatocin ya zame kansa, ya koma bayan Ganduje
Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya caccaki gungun yan majalisar dokokin tarayya da suka kai kararsa hedkwatar jam'iyyar APC kan yadda yake kama karya a jihar.
Ganduje ya bayyana hakan yayinda ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Jiha tare inda ya kaddamar da kwamitocin zaben Shugabannin jam’iyyar a matakin Jiha
An yi wannan taro ne a dakin Africa House dake Gidan Gwamnatin jihar.
A cewar hadimin daukar hoton Ganduje, Aminu Dahiru, yace maigidansa ya kafa hujjoji daban-daban da suka tabbatar da ba'a yin komai a Jam’iyya ba tare da tuntubar yan tawayen ba
Ganduje ya ce:
"Kun gaza yiwa al'ummar mazabunku aiki kuma kuna fuskantar matsala sannan ku fara tuhumata kan matsalolin da kuke fuskanta?"
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Kudinda kuke karba a Abuja al'ummarku basu sha romon ba, sannan kuna daura min laifi?"
Kabiru Gaya ya zame kansa daga cikin wadanda suka kai kara Abuja
Sanata Kabiru Gaya, wanda ke cikin Sanatocin da suka kai karar Ganduje Abuja, ya zame kansa daga lamarin.
Ya bayyana cewa ya cire kansa daga cikinsu Shekarau ne saboda ba zai yi fada da gwamnan da ya taimaka masa ya zama Sanata ba, rahoton DailyNigerian.
Gaya yace ba zai yiwa kansa adalci ba idan ya shiga cikin gungun masu kai karar gwamna.
Ya yi kira ga Sanata Shekarau da sauran yan majalisan su baiwa Ganduje hakurin tawayen da suka masa.
Sanatoci 3, yan majalisar wakilai 4, sun hada kai don kwace mulkin APC hannun Ganduje
Sanatocin dake wakilatar jihar Kano gaba daya da wasu yan majalisar dokokin tarayya sun hadu a gidan tsohon gwamnan jihar Kano dake birnin tarayya Abuja.
Sanatocin dake hallare sun hada da Kabiru Gaya (APC-Kano ta Kudu), Ibrahim Shekarau (APC-Kano ta tsakiya) da Barau Jibrin (APC-Kano ta Arewa)
Mambobin majalisar sun hada da Shugaban kwamitin tsaro na majalisar Sha’aban Sharada (APC-Kano Municipal), Tijjani Jobe (APC-Dawakin Tofa/Tofa/Rimingado); Haruna Dederi (APC-Karaye/Rogo) and; Nasiru Auduwa (APC-Gabasawa/Gezawa).
Asali: Legit.ng