ASUU: Ngige ya Zuga Muguwar Karya, Babu Taron Da Aka Gayyacemu Ranar Alhamis

ASUU: Ngige ya Zuga Muguwar Karya, Babu Taron Da Aka Gayyacemu Ranar Alhamis

Kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'in, ASUU, tace gwamnatin tarayya bata gayyaceta wani taro ba a ranar Alhamis.

A ranar Laraba da ta gabata, Chris Ngige, ministan kwadago da aikin yi, yace gwamnatin tarayya nan babu dadewa za ta kawo karshen yajin aikin da ASUU ta tsunduma watanni hudu da suka gabata.

Ya kara da cewa, matsalolin bangaren biyan albashi da salon da gwamnatin tarayya ta zo da shi wanda kungiyar bata aminta da shi ba duk za a shawo kan shi a taron da za ta yi da kungiyar a ranar Alhamis.

Ministan Kwadago da Ayyukan Yi, Chriss Ngige
ASUU: Ngige ya Zuga Muguwar Karya, Babu Taron Da Aka Gayyacemu Ranar Alhamis. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin zantawa da Sunrise Daily, wani shirin gidan talabijin na Channels a ranar Juma'a, Emmanuel Osodeke, shugaban ASUU, yace kungiyar bata samu wata wasikar gayyata ba daga ministan. Yace Ngige ya cire kanshi daga wannan sasancin saboda ministan kara lalata lamarin yake yi.

Kara karanta wannan

FG Tana Gayyatar Kwararrun Ma'aikatan Gwamnati Da Su Nemi Gurbin Akanta Janar

"Ba a gayyacemu wani taro ba. Babu mambanmu da aka gayyata. Muna da sakateriya amma ba mu samu gayyata daga wurinsu ba," yace.
"Matsalar da muke da ita da gwamnatin nan, ballantana ministan kwadago, shine idan zaka iya zabga karya kace za mu yi taro, ta yaya za mu yarda da wasu abubuwan?
"Ya tabbatar wa da duniya cewa ya gayyace mu taro ranar Alhamis. "Ministan kwadago ya fita daga wannan harkar, ya bar mu da ministan ilimi. Shine ya tabarbara lamarin har ya kai haka. Shi ne ya yanke hukuncin a yi amfani da yunwa matsayin makami, lokacin da yace in har bamu koma bakin aiki ba, ba za a biya mu ba."

Babu Dadewa Daliban Jami'o'i Zasu Koma Aji, FG

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ana dab da komawa karatu nan babu dadewa saboda yadda ta mayar da hankali wurin shawo kan matsalolin kungiyoyin jami'o'i.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Yajin-aikin Kungiyar ASUU ya kusa zama tsohon labari - Gwamnatin Buhari

Kungiyar malaman jami'o'i msau koyawa, ASUU, Kungiyar ma'aikatan jami'o'in da basu koyarwa, NASU da Kungiyar Manyan ma'aikatan jami'o'in Najeriya, SSANU duk suna yajin aiki.

A yayin jawabi a taron majalisar zartarwa ta tarayya, FEC wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadarsa dake Abuja, ministan kwadago da aikin yi, Sanata Chris Ngige, ya ce ana hangon karshen yajin aikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel