Majalisar dokokin Filato ta ayyana kujerar kakakin da ta tsige da bakowa kan ya koma PDP

Majalisar dokokin Filato ta ayyana kujerar kakakin da ta tsige da bakowa kan ya koma PDP

  • Majalisar dokokin jihar Filato ta bayyana kujerar tsohon kakakinta da bakowa saboda ya koma jam'iyyar PDP
  • Kakakin majalisar, Yakubu Sanda, ya ce sun samu wasika daga shugaban APC na jiha kan matakin da tsohon kakakin ya ɗauka
  • Tsohon kakaki, Abok Ayuba, ya miƙa takaradar ficewa daga APC tare da komawa PDP a karamar hukumarsa da Jos East

Plateau - Majalisar dokokin jihar Filato dake arewa maso tsakiya a Najeriya ta bayyana kujerar tsohon kakakin majalisa da mambobi suka tsige, Abok Ayuba, da ba kowa.

Daily Trust ta rahoto cewa Kakakin majalisar, Yakubu Sanda, shi ne ya bayyana haka a zaman su na yau Talata, 22 ga watan Maris, 2022.

Honorabul Sanda ya ce sun ɗauki wannan matakin ne biyo bayan wasikar da shugaban APC na jihar ya aiko wa majalisar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta gamu da babbar matsala, wani jigo tare da dandazon masoya sun koma PDP

Tsohon kakakin Filato
Majalisar dokokin Filato ta ayyana kujerar kakakin da ta tsige da bakowa kan ya koma PDP Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Shugaban APC ya yi bayanin cewa tsohon kakakin ya aika wa jam'iyya hukuncin da ya yanke na ficewa daga APC tare da komawa PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin majalisar ya ce sun bayyana kujerarsa da ba kowa ne saboda ficewa daga APC ba tare da kwakkwaran dalilin rikici da jam'iyya ke fuskanta ba.

Yaushe ya koma PDP?

Da yake miƙa takaradar sauya shekarsa zuwa PDP a Sakatariyar jam'iyyar dake Angware, ƙaramar hukumar Jos East, tsohon Kakakin ya ce natakin ya zama tilas a kansa.

A cewarsa, wajibi ne ya ceto ƙaramar hukumarsa da jiha baki ɗaya daga mulkin kama karya dake shirin ruguza Filato baki ɗaya idan aka yi sake.

Ya kuma yaba wa jam'iyyar PDP bisa amince masa ya dawo gida da kuma kyakkyawar tarban da aka masa.

Leadership ta rahoto A kalamansa ya ce:

Kara karanta wannan

2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP

"Ina tsaye a gabanku ne da tsantsar farin ciki da kalaman amince mun da kuka yi na dawo."

Wannan shi ne karo na farko da kakakin wata majalisar dokoki ya bayyana kujera da babu kowa sabida sauya sheka daga wata jam'iyya zuwa wata.

A wani labarin kuma 'Zan cika burin yan Najeriya' Matashi dan shekara 45 ya shiga tseren gaje kujerar Buhari a 2023

Matashi ɗan shekara 45 daga jihar Osun yace lokaci ya yi matasa zasu fito su karbi ragamar mulkin Najeriya.

Mista Joseph, wanda ya bayyana shiga tseren takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya a 2023, ya ce ya shirya tsaf domin kawo canji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel