Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta yi amai ta lashe, tace Gwamna Mala Buni ne shugaban riko
- Jam'iyyar APC ta yi gaba kuma ta dawo baya, ta canza magana, tace har yanzun gwamna Buni ne shugaban kwamitin riko
- Kakakin kwamitin rikon kwarya na APC ta kasa, Ismaeel Ahmed, yace bai san mai yasa mutane suak fahintar lamarin ba
- Yace tun sanda aka kafa kwamitin rikon kwarya a 2020, duk lokacin da Buni baya nan gwamna Bello ne ke maye gurbinsa
Abuja - Kwamitin rikon kwarya (CECPC) na jam'iyyar APC ya ce har yanzun gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ne shugaba, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Wasu daga cikin gwamnonin APC sun nuna goyon bayan su ga gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, wanda ya karbi jagorancin kwmaitin ranar Litinin.
Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, yace gwamna Buni wanda ya tafi Dubai domin bincika lafiyarsa, Buhari ya bada umarnin cire shi daga shugabanci.
Ya kuma zargi Buni da ƙara rura wutar rikicin APC a cikin gida, inda ya kara da cewa cire Buni alkairi ne kuma tuni Abubakar Bello ya karbi jagoranci da goyon bayan gwamnoni 19.
Da yake jawabi ga manema labarai a Sakatariyar APC ta ƙasa dake Abuja, Kakakin (CECPC), Ismaeel Ahmed, ya ce ya gaza gane meyasa lamarin ke ruɗa wasu mutane.
Vanguard ta rahoto Ya ce:
"Wani ya tambaye ne menene makomar Mala Buni a jam'iyya, inaga wannan abu ne mai sauki, ban san meyasa mutane da yawa suka gaza fahimta ba."
"Tun da aka kafa kwamitin rikon kwarya ranar 25 ga watan Yuni, 2020, duk lokacin da shugaba baya nan, gwamna Bello ke wakiltarsa. Wannan ne abin da ke faruwa tun farko.
"Muna da babban taro ranar 26 ga watan Fabrairu, Buni ya rubuta wasikar damka mulki a hannun Bello domin ya tafi duba lafiya. Abu ne na gaggawa da ya shafi lafiya. Mu kuma muna da babban taro, ba zamu jira har sai ya samu lafiya ba."
Meyasa Abubakar Bello ya karbi jagorancin APC baki ɗaya?
Ahmed ya ƙara da cewa kasancewar shugaba baya nan, gwamna Bello ya karbi cikakken ragamar tafiyar da APC kuma nauyin komai ya koma kansa.
"Abu ne mai sauki kuma a bayyane, idan akwai wanda lamarin be masa daɗi ba, yana da damar zuwa Kotu. A yanzu muna tafiyar da harkokin mu ne kan doka, dan haka babu wani rashin tabbas."
A wani labarin kuma Bola Tinubu ya keɓe da da gwamna Umahi dake neman takarar shugaban ƙasa a 2023
Jagoran jam'iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu da kuma gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, sun gana da juna a babban birnin tarayya Abuja, ranar Jumu'a.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwar da hadimi na musamman na gwamnan jihar Ebonyi , Francis Nwaze, ya fitar a shafinsa na dandalin sada zumunta.
Asali: Legit.ng