Gwamna Matawalle ya gargaɗi gwamnoni abu daya game da rikicin jam'iyyar APC

Gwamna Matawalle ya gargaɗi gwamnoni abu daya game da rikicin jam'iyyar APC

  • Gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya gargaɗi gwamnonin APC kan kalaman wuce gona da iri game da rikicin cikin gida
  • Gwamnan ya ce kowane daga cikinsu na taka rawa wajen cigaban APC, kuma haka gwamna Buni, ya yi matukar kokari
  • Matawalle ya yaba wa shugaban ƙasa Buhari Buhari bisa kama girmansa da taka rawar Uba a harkokin APC

Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya gargaɗi takwarororinsa gwamnoni kan kalaman wuce gona da iri game da rikicin shugabancin jam'iyyar APC.

Matawalle ya yi wannan gargadin ne a wata sanarwa da kakakinsa, Zailani Bappa, ya fitar ranar Jumu'a a Gusau, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle
Gwamna Matawalle ya gargaɗi gwamnoni abu daya game da rikicin jam'iyyar APC Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A sanarwan, gwamna Matawalle ya ce:

"Ba dai-dai bane mu rinka sakin baki a kafafen watsa labarai, musamman a lokaci mai wahala da jam'iyyar mu ke fuskanta, yayin da muke fuskantar zaɓen 2023."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta yi amai ta lashe, tace har yanzu Gwamna Mala Buni ne shugabanta

"Na yi imanin cewa kowannen mu na iya bakin kokarinsa wajen matsar da jam'iyya gaba. Ba bu tantama Gwamna Mala Buni ya ba da gudummuwa wajen cigaban APC, haka nan kuma sauran gwamnoni, duk da akwai sabani."
"Haka demokaradiyya take, amma ba bu wani gurbi da zamu dawo da sabanin dake tsakanin mu, bayan kowa ya maida wukarsa an samu maslaha."

Ku daina saka Buhari a cikin wannan lamarin - Matawalle

Gwamnan ya ƙara da cewa bai kamata ma su magana kan lamarin su rinka sanya sunan shugaba Buhari a ɓangare ɗaya ba.

"Ba bu waye wa a saka sunan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ɓangare ɗaya na lamarin da ya saba faruwa, saɓani ne na siyasa da aka saba gani a duk inda aka haɗa ra'ayoyi mabanbanta."

Kara karanta wannan

Tsige Mala Buni: Gwamnoni 2 da Minista sun garzaya Landan, za su sa labule da Buhari

"Yanzun lokaci ne da jam'iyya ke bukatar ƙara karfi da haɗin kai domin fuskantar dukkan kalubale dake gabanin babban zaɓe mai muhimmanci, wajibi APC ta rike nasararta a kowane mataki."

Matawalle ya kuma yaba wa shugaban ƙasa Buhari bisa taka rawar Uba kuma jagora a dukkan abinda ya shafi harkokin jam'iyya, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Ya kuma yaba wa takwarorinsa gwamnoni bisa gudummuwar da suka bayar wajen nasarar da jam'iyya mai mulki ke samu.

A wani labarin kuma Shugaban PDP na ƙasa ya ce Gwamna Obaseki na nan daram a PDP, jam'iyya ta riga ta yi ram da shi

Shugaban PDP na ƙasa ya kori duk wani raɗe-raɗin dake yawo cewa gwamnan Edo zai fice daga jam'iyyar ya koma APC.

Sanata Ayu ya ce ba inda gwamna Obaseki zai je, kuma PDP zata kafa kwamitin da zai magance saɓanin dake cikin PDP a jihar..

Kara karanta wannan

Mai Mala bai bani wata wasika ba: Gwamna Neja ya yi martani mai zafi

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262