Rarara Ya Faɗi yadda Ya Gawurta a Waka maimakon Gadon Karatun Kur'ani
- Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya bayyana cewa nadin Sarkin wakar kasar Hausa da aka yi masa ya zame masa muhimmin abu a rayuwarsa
- Shahararren APC ya ce wannan matsayi ya wuce duk wata girmamawa da ya taba samu a baya, inda ya jinjina yadda Shugaban Kasa ya san shi kai tsaye
- Rarara tuna yadda aka dauko shi daga Kahutu a jihar Katsina zuwa Kano domin neman ilimi, inda ya bayyana cewa mahainsa ya gama nuna shi a matsayin magaji
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Fitaccen mawakin Dauda Kahutu Rarara ya bayyana yadda ya ji game da nadin Sarkin wakar kasar Hausa da aka yi masa a baya-bayan nan.
Ya ce ko da iya sanin da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi masa a matsayin mawakinsa, to wannan sabon matsayi ya kure duk wata girmamawa da ya taba samu.

Source: Facebook
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Rarara ya bayyana cewa sarautar wakar kasar Hausa na haska masa wani abu na musamman a rayuwarsa.
Yadda Rarara ke kallon nadin sarautarsa
Dauda Kahutu Rarara ya ce wannan sarauta ta zo masa ne a matsayin wata babbar alama da ke nuna girman abin da ya cimma a rayuwa.
Fitaccen mawakin na APC ya bayyana asalinsa almajiri ne da yayansa ya dauko shi a mota daga Kahutu a jihar Katsina zuwa Kano domin neman karatu.
Ya ce:
"A wannan da'irar da na ke ciki, ko 'dan rukunin da na ke ciki, ai babu abin da ya fi wannan sarauta, waka na ke yi, yau aka ce ni ne sarkin mawaka na kasar Hausa gaba daya."
"Ni dai ban ga wani abu da ya fi wannan ba, duba da yadda na taso."
Rarara ya magantu kan gadar mahaifinsa
Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa bai gaji waka daga wajen mahaifinsa ba, domin a cewarsa karatun Kur’ani aka fi so ya zama ginshiki a rayuwarsa.

Source: Facebook
Ya ce:
"Yanzu akwai abokan babana da idan aka ce masu ni ne na ke waka, sai ya ce Allah Sarki. Allah mai yadda ya so."
"Saboda duk inda babanmu za shi da ni, a matsayin ni ne magajin gida ya ke magana."
Rarara ya kara da cewa mahaifinsa ya yi tsammanin shi ne zai gaji gidansu, ganin yadda aka yi karatu da mahaddata da marubutan Al’Kur’ani mai tsarki a gidansu.
Ya kara da cewa daga cikin almajiransa, an samu wadanda suka rubuta Al Kur'ani mai tsarki, saboda haka aka yi tsammanin shi ma zai gaji gida.
Rarara: An mika bukata ga Nyesom Wike
A baya, mun wallafa cewa wani masoyin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Khamis Musa Darazo, ya miƙa buƙatarsa ga Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, kan batun Dauda Kahutu Rarara.
Khamis Musa Darazo ya yi kira ga Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, da ya sanya sunan Dauda Kahutu Rarara a wani titi a Abuja domin girmama gudunmawar da ya bayar a fannin al’adu da siyasa.
A cewarsa, wannan mataki zai zama wata babbar hanya ta nuna godiya ga rawar da Rarara ya taka wajen ƙarfafa siyasa da haɗin kan al’umma ta hanyar waka da gudunmawarsa ga gwamnatin Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

