Bayan Sanar da Dakatar da Shi, Sakataren PDP Ya Nema wa Kansa Mafita a Jam'iyya

Bayan Sanar da Dakatar da Shi, Sakataren PDP Ya Nema wa Kansa Mafita a Jam'iyya

  • Barakar da ta ratsa cikin jam'iyyar adawa PDP na kara bayyana a jihar Kaduna bayan ta dakatar da sakatarenta na jihar Kaduna
  • Sanarwar da PDP ta fitar ce ta tabbatar da dakatar da Sa’idu Adamu, bisa zargin saba wa doka da ayyukan cin amanar jam’iyya
  • PDP ta ce an dakatar da Sa'idu na tsawon wata guda yayin da ake ci gaba da bincike kan laifuffukan da ake zargin ya aikata

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta sanar da dakatar da Sakataren jam’iyya na jiha, Hon. Sa’idu Adamu.

Jam'iyyar adawa a Kaduna ce an dakatar da Sa'idu bisa zargin aikata manyan laifuffuka da kuma gudanar da ayyukan cin amanar jam’iyya.

Kara karanta wannan

Kano: 'Dan jarida ya debo ruwan dafa kansa, ICPC ta kama shi kan zambar N14m

PDP ta kara fada wa a cikin rikici
Hoton Shugaban PDP na kasa, Ambasada Damagum Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wannan mataki na nuna yadda rikicin cikin gida ke kara tsananta a cikin jam’iyyar adawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar PDP ta dakatar da sakatarenta

Channels TV ta wallafa cewa a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar a jihar, Hon. Maria Dogo, ta tabbatar da dakatar da Sa'idu Adamu.

Ta bayyana cewa Kwamitin Gudanarwa na Jiha ya amince da dakatarwar a taron da aka gudanar a ranar Litinin, 6 ga Oktoba, 2025 a hedkwatar jam’iyyar da ke Kaduna.

Sanarwar ta ce an dauki matakin ne bisa tanade-tanaden dokar jam’iyyar PDP, sashe na 58(1)(h) da 57(3) na kundin tsarin mulki na shekarar 2017 (wanda aka gyara).

Ta ce wadannan sassa sun bai wa jam’iyya damar ladabtar da duk wanda ke aikata abin da zai cutar da jam’iyyar ko hadin kan ta.

An dakatar da sakataren PDP na wata daya

Jam'iyyar PDP, reshen jihar Kaduna ta bayyana cewa an dakatar da Sa’idu Adamu na tsawon wata guda, kuma hakan zai fara aiki nan take.

Kara karanta wannan

Ana batun kisan kiyashin Kiristoci, CAN ta aika sako ga gwamnatin tarayya

An dakatar da sakataren PDP a Kaduna
Hoton taswirar jihar Kaduna, inda PDP ke fama da rikici Hoto: Legit.ng
Source: Original

A wannan lokacin, ba zai halarci ko wani taron jam’iyya a matakin ƙasa ko jiha ba, har sai an kammala bincike da yanke hukunci daga uwar jam’iyya.

A daidai lokacin da labarin dakatarwarsa ke yawo, wani faifan bidiyo ya bayyana a kafafen sada zumunta inda Sa’idu Adamu ke sanar da murabus daga PDP baki daya.

A cikin bidiyon, Adamu ya bayyana abubuwan da suka faru a wani taro da aka gudanar a gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi, wanda shi ma jigo ne a PDP.

Taron ya haɗa da ɗan takarar gwamna na PDP a 2023, Isa Ashiru, da shugaban jam’iyya na jiha, Edward Percy Masha, inda ya ce rashin jituwa tsakaninsa da Isa ya sa ya bar PDP.

Ya ce:

“Na yanke shawarar yin murabus daga matsayi na da kuma daga jam’iyya. Daga yau, ba ni da alaƙa da PDP. A cikin kwanaki masu zuwa, zan bayyana sabuwar jam’iyyar da zan shiga bayan na tattauna da jama’ata.”

Kara karanta wannan

NYSC: Jerin ministoci 6 da suka shiga badakalar takardun bogi a Najeriya

Jam'iyyar PDP ta yi rashin Sanata

A baya, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta PDP reshen jihar Edo ta yi babban rashi, bayan da tsohon sanata, Ehigie Uzamera, ya sanar da murabus daga cikinta baki daya.

A cikin wasiƙar da ya aika wa shugaban jam’iyyar a mazaba ta 12, Karamar Hukumar Ovia ta Arewa, Uzamera ya bayyana cewa ficewarsa ba ta haifar da barazana, rikici ko sabani ba.

Ya ce ya yanke shawarar canza jam’iyya ne saboda neman wata madogara da za ta ba shi dama ya ci gaba da hidimta jama’arsa yadda ya kamata a cikin kwanciyar hankali.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng