An Kammala Shirin BBNaija 2025, Matashiya 'Yar Shekara 23 Ta Lashe Kyautar N150m

An Kammala Shirin BBNaija 2025, Matashiya 'Yar Shekara 23 Ta Lashe Kyautar N150m

  • Opeyemi ‘Imisi’ Ayanwale ta zama zakarar gasar Big Brother Naija zango na 10, inda ta lashe kyautar Naira miliyan 150
  • Imisi ta samu 42.8% na kuri’un masu kallo, yayin da ta doke Dede, ya zo na biyu da 15.94%, sannan Koyin ya zo na uku da 15.23%
  • 'Yar shekara 23 daga jiyar Oyo, Imisi ta zama abin so ga masu kallo saboda halayenta na barkwanci, iya magana da juriyarta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - ‘Yar wasan kwaikwayo mai barkwanci kuma mai faɗin albarkacin baki, Opeyemi ‘Imisi’ Ayanwale, ta lashe gasar Big Brother Naija kashi na 10.

Imisi ta zama zakar gasar ta bana, inda ta tashi da kyautar Naira miliyan 150 — mafi girman kudin da aka taba samu a tarihin shirin.

Kara karanta wannan

A mako 1 kacal, farashin gas ɗin girki ya ƙaru da N7,500 a Legas da wasu jihohi

Opeyemi 'Imisi' Ayanwale ta zama zakarar gasar BBNaija zango na 10, ta samu kyautar N150m
Hoton Opeyemi 'Imisi' Ayanwale, matashiyar da ta lashe gasar BBNaija zango na 10. Hoto: @Opybobo_OfLagos/X
Source: Instagram

Imisi ta lashe N150m a gasar BBNaija

Imisi ta samu 42.8% na kuri’un masu kallo, ta doke Dede wanda ya zo na biyu da 15.94%, da Koyin wanda ya zo na uku da 15.23%, inji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran ‘yan wasa da suka biyo bayansu sun hada da Sultana (7.94%), Kola (5.48%), Jason Jae (4.84%), Mensan (3.54%), Isabella (3.07%) da Kaybobo (1.72%).

Imisi ta zama abin so ga masu kallo saboda halayenta na barkwanci, iya magana cikin hikima, da yadda take kame kanta daga hayaniya a lokutan tashin hankali.

“Ijoba 606,” sunan da masoyanta ke kiran kanta da shi, ta nuna juriya da gaskiya a cikin gidan Big Brother, abin da ya sa ta zama mafi soyuwa ga masu kallo.

Abin da ya sa Imisi ta lashe gasar BBNaija

A cikin makonni 10 na shirin, Imisi ta yi daban da sauran 'yan wasa, ta fuskar nuna halayen barkwanci, gaskiya, da kwazo.

Kara karanta wannan

Tirelar siminti ta murkushe Keke Napep, fasinjoji 5 da ke ciki sun mutu nan take

Ta kasance mai natsuwa ko da a lokacin da kowa ke cikin fargaba, tana kuma kere sa'a a tsakanin sauran ‘yan gidan da kalamai masu sanya dariya.

Yayin da shirin BBNaija zango na 10 ya zo karshe, an umarci Koyin ta fita daga gidan, lamarin da ya rage saura Dede da Imisi, wadanda suka je zagayen karshe.

Bayan kada kuri'ar karshe, Imisi ta zamo zakarar gasar Big Brother ta bana, lamarin da ya jefa masoyanta cikin farin ciki, da cewar 'tamu ta samu,' inji rahoton Channels TV.

Kamar yadda al’adar shirin ta tanada, an kashe fitilu a gidan bayan ficewar Imisi da Dede, abin da ya sanya damuwa ga masoya da suka shafe makonni suna kallon shirin.

An kammala shirin BBNaija zango na 10 cikin nishadi, inda Imisi ta lashe gasar
Hoton tambarin shirin Big Brother Naija, wanda ake yinsa kai tsaye a Najeriya. Hoto: @oluwatoyinbola/X
Source: UGC

Bikin karshe na shirin BBNaija zango na 10

Bikin karshe wanda Ebuka Obi-Uchendu ya jagoranta ya gudana cikin shagali, inda fitattun mawaka kamar Adekunle Gold da Iyanya suka nishadantar da jama’a.

Shirin wanda ya fara a 26–27 ga Yuli, 2025, ya kunshi ‘yan wasa 29 daga Najeriya da wasu ƙasashe, inda aka ga rikice-rikice, soyayya, abubuwan dariya, da na hawaye da suka ja hankalin miliyoyin masu kallo a Afirka.

Kara karanta wannan

Tazarce: An zakulo manyan abubuwa 6 da za su taimaka wa Tinubu ya ci zabe a 2027

Imisi yanzu ta shiga jerin fitattun zakarun Big Brother Naija da rayuwarsu ta sauya saboda wannan shiri, tare da sababbin damarmakin kasuwanci, da mabiya a shafukan sada zumunta.

'Yan Arewa sun shiga BBNaija 10

Tun da fari, mun ruwaito cewa, matasan 'yan mata uku daga Arewacin Najeriya ne suka shiga shirin BBNaija zango na 10 da aka gudanar a 2025.

Daga cikin mata 15 da suka shiga gasar ta bana, mata uku sun fito ne daga jihohin Arewa; Kaduna, Benue da kuma Adamawa - abin da ba a saba gani ba.

Sonia Amako, wadda aka rika kiranta da Big Soso a shirin ta fito ne daga Kaduna, yayin da Farida Sultana Auduson Ibrahim ta fito daga jihar Adamawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com