‘Samu Na Ya Ƙaru’: G Fresh Ya Faɗi Miliyoyin da Yake Samu a TikTok bayan Aure
- Dan TikTok, G-Fresh Al’ameen ya ce bai ga matsala a bidiyonsa ba duk da korafe-korafen mutane, kuma samun kudinsa ya karu bayan aure
- Ya bayyana cewa kafin aure yana samun N2m a wata daga TikTok, yanzu kuwa kudin ya ninka adadin ko ma fiye da haka
- Matarsa, Maryam Ahmad Yola ta ce tana fuskantar kalubale saboda jama'a na gane ta a ko’ina, duk da cewa bata ga matsala a bidiyonsa ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Fitaccen dan TikTok a Najeriya, Abubakar Ibrahim ya yi magana kan rayuwa da kuma kalar bidiyo da yake yi.
G-Fresh Al’ameen ya bayyana cewa shi bai ga komai na rashin kyautawa ba game da irin bidiyon da yake yi wanda mutane ke korafi.

Asali: Facebook
G-Fresh Al'ameen ya magantu kan nasarorinsa

Kara karanta wannan
Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5
Dan TikTok din ya bayyana haka ne yayin hira da BBC Hausa a cikin shirinsu na mahangar zamani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce shi kansa bidiyon soki-burutsu da yake yi yana ba shi nishadi ba ma al'ummar Najeriya ba saboda bai son zama haka banza.
G-Fresh ya kuma yi karin haske kan karuwar da yake samu ta fannin kudin shiga bayan ya auri matarsa daga jihar Adamawa.
Ya ce kafin ya auri abar kaunarsa yana samun abin da bai wuce N2m ba TikTok amma bayan ya aure ta ya samu ninkin haka.
Ya ce:
"Tun da na aure ta ba ma Abuja ba, gaskiya samu na ya karu a kafofin sadarwa musamman a TikTok.
"Ina cire kaman N2m a wata a TikTok kafin na aure ta amma yanzu abin da nake samu a TikTok ya kai N4m ko fiye da haka, ta ninka mani abin da na ke samu gaskiya."

Asali: Facebook
Matar G-Fresh ta yaba halayen dan TikTok
Har ila yau, matar G-Fresh, Maryam Ahmad Yola ta yi magana kan kalubale ta take samu a matsayinta na mai dakin dan TikTok din.
Ta ce:
"Gakiya akwai wasu kalubale saboda ko na fita kasuwa ko da na saka 'face mask' za a rika cewa ga matar G-Fresh.
"Ban ga wata matsala a cikin bidiyo da yake yi ba saboda idan zai yi na tsalle-tsalle bai sani a ciki saboda zai iya harbina da kafa, Gaskiya da zai daina kam ina so."
Maryam ta kuma bayyana yadda take jin dadi da zama da shi saboda mutum ne wanda bai yin fushi kuma yana kula da ita sosai.
An tura G-Fresh zuwa gidan yari
A baya, mun ba ku labarin cewa shahararren dan TikTok daga Kano, Abubakar Ibrahim (G-Fresh) ya shiga matsala bayan kotu ta same shi da laifin cin zarafin Naira a jihar.
Kotun tarayya ta tasa keyarsa zuwa gidan gyaran hali ko ya biya tara N200,000 bayan ya amsa laifinsa ba tare da wani bata lokaci ba.
An zargi G-Fresh da cin mutuncin Naira a shagon yar TikTok mai suna Rahama Sa’idu da ke Tarauni da ke birnin Kano wanda ya jawo masa matsala.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng