'Zan Aure Ta': Fitaccen Mawakin Najeriya Ya Kamu da Soyayyar 'Yar Majalisa
- Mawakin Najeriya, Innocent Idibia, ya sanar da alakar soyayyar da ke tsakaninsa da ‘yar majalisar jihar Edo, Natasha Osawaru
- Natasha, mataimakiyar shugaban masu rinjaye a majalisar Edo, ta ja hankalin mutane bayan bullar hotuna da bidiyoyinta da 2Baba
- A cikin bidiyon da ya yadu, 2Baba ya ce Natasha ba ta da alaka da rabuwarsa da Annie Idibia kuma yana son 'yar majalisar da aure
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Shahararren mawakin Najeriya, Innocent Idibia, watau 2Baba, ya bayyana Natasha Osawaru a matsayin sabuwar budurwarsa.
2Baba ya sanar da alakar da ke tsakaninsa da 'yar majalisar ne kwanaki 16 bayan sanar da rabuwa da matarsa, Annie Macaulay.

Asali: Twitter
Mawaki, 2Baba ya ziyarci 'yar majalisa
Natasha Osawaru, mataimakiyar shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Edo, lamarin da ya ja hankalin mutane sosai, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Labari kan alakar mawakin da ‘yar siyasar ya mamaye kafafen sada zumunta bayan hotuna da bidiyoyi sun bayyana kafin sanarwar rabuwa da Annie.
A ranar Litinin, mawaki 2Baba ya ziyarci zauren majalisar jihar Edo yayin zaman majalisar, lamarin da ya kara tabbatar da jita-jitar dangantakarsu.
Mawaki na shirin auren 'yar majalisar Edo
A ranar Talata, 2Baba ya tabbatar da jita-jitar yayin da ya bayyana soyayyarsa ga Osawaru a cikin wani bidiyo da ya kara yaduwa.
A cikin bidiyon, ya ce:
“Hon. Natasha ba ta da alaka da matsalolin aurena da Annie, kuma ba ita ce silar rabuwarmu ba. Ita mace ce ta musamman, kuma ina sonta sosai.”
2Baba ya kara da cewa ya yanke shawarar auren ‘yar siyasar saboda kyawawan halayenta, duk da cewa mutane na ta yada cewa ita ta rusa aurensa.
Premium Times ta rahoto cewa kamar bidiyon sanar da rabuwa da Annie, mawakin ya goge bidiyon sanarwar shirin aurensa da Natasha bayan ya yadu a intanet.
Mawaki 2Baba ya saki matarsa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shahararren mawakin Najeriya, Innocent Idibia (2Baba), ya rabu da matarsa, Annie Idibia, bayan zaman shekara 12.
A halin yanzu, tsofaffin ma’auratan sun daina bin juna a shafukan sada zumunta, lamarin da ya kara tabbatarwa duniya da rabuwar tasu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng