Hotuna: Fitaccen Mawakin Siyasa, Rarara Ya Bude Sabon Gidan Biredi a Jihar Katsina

Hotuna: Fitaccen Mawakin Siyasa, Rarara Ya Bude Sabon Gidan Biredi a Jihar Katsina

  • Mawakin siyasa Dauda Rarara ya kai ziyara Kahutu, jihar Katsina, inda ya duba aikin masallacin Juma'ah da yake ginawa
  • A yayin ziyarar, Rarara ya ziyarci sabon gidan biredinsa mai suna Mama Bread, tare da abokinsa Abdullahi Alhikima
  • Hotuna sun nuna Rarara da Alhikima suna cin biredi cikin nishadi a gidan biredin da ya bude a karamar hukumar Danja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Adamu Abdullahi ya ziyarci gidan biredi da ya bude a mahaifarsa ta Kahutu da ke Danja, jihar Katsina.

A ranar Asabar ne aka ce jami'ar waka, Dauda Rarara ya kai ziyara a garin Kahutu tare da tawagarsa, ciki har da abokinsa, Abdullahi Alhikima.

Mawaki Rarara ya magantu yayin da ya ziyarci gidan biredinsa da masallacin da yake ginawa a Katsina
Dauda Kahutu Rarara ya ziyarci gidan biredin da ya bude da masallacin da yake ginawa a Katsina. Hoto: Rabi'u Garba Gaya
Asali: Facebook

Rarara ya ziyarci masallacin da yake ginawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabi'u Garba Gaya, mai magana da yawun mawakin ya sana a shafinsa na Facebook cewa Rarara ya ziyarci Kahutu domin duba masallacin Juma'ah da yake ginawa.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yanke shawara bayan jami'an tsaro sun hana shi zuwa Bichi

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa mawaki Rarara ya kaddamar da gina masallacin Naira miliyan 350 a garin Kahutu, jihar Katsina.

A ziyarar da ya kai ranar Asabar, mawakin ya zagaya inda ake ginin masallacin domin ganewa idonsa yadda aikin ke gudana.

Hotuna sun nuna matakin da ginin masallacin ya kai, wanda ya zama abin magana da jinjina ga mawaki Rarara a shafukan sada zumunta.

Kalli hotunan a kasa:

Mawaki Rarara ya bude sabon gidan biredi

Bayan kammala ziyarar masallacin da yake ginawa, an ce mawaki Rarara tare da Abdullahi Alhikima da tawagarsa sun garzaya sabon gidan biredi da ya bude a garin.

A cikin gidan biredin, Rabi'u Gaya ya wallafa hotunan mawakin da Alhikima suna cin biredi cike da nishadi da kuma tattaunawa kan yanayin aikin gidan biredin.

Rabi'u Gaya ya wallafa cewa:

"Rarara ya ziyarci gidan biredinsa mai suna Mama Bread shi da abokinsa Abdullahi Alhikima wanda yake a garin Kahutu da ke karamar hukumar Danja, jihar Katsina."

Kara karanta wannan

Hotuna: Fitaccen mawakin siyasar Arewa, Rarara ya fara gina sabon masallaci a Kano

Kalli hotunan a kasa:

Rarara ya fara gina masallaci a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa mawakin siyasa, Abdullahi Kahutu Rarara ya amsa rokon jama'ar garin Kuduri da ke cikin karamar hukumar Sumaila, jihar Katsina.

Al'ummar garin Kuduri sun roki Rarara ya gina masu masallaci bayan wanda suke da shi ya rushe sanadin ruwan sama, inda mawakin ya kaddamar da gina masu sabo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.