Murja Kunya: Mutane Sun Yi Ca yayin da Fitaccen 'Yar TikTok Ta Sayi iPhone 16
- Fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya ta bude sabuwar wayar kamfanin Apple, watau iPhone 16 daga cikin kwalinta
- Murja Kunya ta shaidawa masoyanta cewa ba a shagon mai sayar da waya ta bude iPhone din ba balle ayi tunanin duk 'buge ce'
- Yayin da aka wallafa hotunan Murja rike da sabuwar iPhone 16 da ta saya, 'yan soshiyal midiya sun yi mata ca kan sayen wayar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Har yanzu dai ba a kammala yayin wayar kamfanin Apple da ta fito kwanan nan, watau iPhone 16 a masana'antar nishadi ta Arewa ba.
Jarumai da mawakan Kannywood, da kuma fitattun jaruman TikTok na Arewacin kasar na ci gaba da baje kolin iPhone 16 da suka saya.
Murja Kunya ta sayi iPhone 16
Itama fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta saki bidiyo a shafinta na Facebook, inda ta nuna lokacin da ta bare iPhone 16 a kwalinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, an ga jarumar zaune dirshan tana bude sabuwar wayarta yayin da ta take jawabi ga masoyanta cewa, 'ba a shagon masu waya ta bude ta ba.'
Murja Ibrahim Kunya, wacce ta yi kaurin suna a Arewa, tun lokacin da hukumar Hisbah ta cafketa kan yada bidiyon badala a intanet, ta ce:
"Abu gashi kowa ya san tamu ce ba a shagon waya muka bude ta ba."
Mutane sun yiwa Murja Kunya ca
Shafin Arewa Blog ya wallafa hotunan jarumar TikTok, Murja Kunya a shafinsa na Instagram inda take dauke da sabuwar wayar iPhone 16.
Arewa Blog ya wallafa cewa:
"To fa! A karshe dai Murja Kunya ta mallaki iPhone 16."
A karkashin wannan wallafa, mutane sun yiwa jarumar ca.
mutan_kannywood:
"An gama yayin ta a saura GLK."
musty_for_the_ladies:
"Allah ya sa da kudin halak ta siya."
__m.u.b.a.r.a.q__:
"Ita sai yanzu ta ke mallaka, ai manya manyan sun dade da mallaka"
kheenson:
"Yo ita duk barikin nata sai yanzu ta karbi nata amma dai taba marke kunya wallahi."
Kalli bidiyon a kasa:
Kotu ta dauki mataki kan Murja Kunya
A wani labarin, mun ruwaito cewa babbar kotun jihar Kano ta bayar da belin fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya kan Naira 500,000.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ce ta gurfanar da Murja Kunya gaban kotun bayan kama ta da laifin yada bidiyo da hotunan badala a soshiyal midiya.
Asali: Legit.ng