"Ka da Ka yi Tunanin Aure sai Ka Ajiye N50m,' 'Yar Tiktok ta ba Maza Shawara
- Mai amfani da kafafen sada zumunta Saida BOJ ta ba maza shawarar abin da ya kamata su tanada kafin su fara tunanin aure a wannan zamanin
- Wannan lokacin ta shawarci mabiyanta miliyan 1.3 da cewa bai kamata namiji ya daukowa kansa batun aure ba matukar ya san bai ajiye wasu makudan kudi ba
- Ta ce akalla duk namijin da ke son ya yi aure ya ajiye wata ‘yar 50m, domin aure na da dawainiya da yawa kamar kula da matar da yaran da za a haifa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Nigeria- Wata shahararriyar ‘yar tiktok, Sarah Idaji Ojone ta shawarci maza su daina dauko batun aure idan sun san asusunsu bai cika taf da kudi ba.
An jiyo ‘yar tiktok din da aka fi sani da Saida BOJ ta cikin wani shirin ‘Blessing CEO podcast’ tana cewa akalla kowane namiji na bukatar ya ajiye N50m kafin ya kinkimo batun aure.
Legit.ng ta ruwaito cewa Ojone ta sake nanata matsayarta ga mabiyanta miliyan 1.3 na tiktok jim kadan bayan ta samu dawowa da shafin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa ake son auren namiji da kudi?
Saida BOJ dai ta kafe a kan batun da ta yi na cewa dole sai namiji yana da kudi maganar aure za ta kankama.
Ta zayyano dalilai da dama da yasa take ganin ana bukatar makudan kudin idan har da gaske aure mutum zai yi, kamar yadda Intel Region ta wallafa.
Daga dalilanta, ‘yar tiktok din na ganin dawainiyar yaran da ake sa ran za a haifa, da ita kanta kulawa da matar za su ci kudi ba kadan ba.
Ta ce duk da namiji zai iya yin dace ya samu mace mai fahimtar kowane hali da yake ciki, amma fa ta ce sam bata ba mata shawara su zama masu fahimtar.
Kyauta dillaliya ta tsunduma aikin DJ
A wani labarin kun ji cewa 'yar fim din kannywood, Fatima Nayo da aka fi sani da kyauta Dillaliya ta tsunduma aikin kida a wajen taro wato DJ.
Kyauta Dillaliya ta bayyana cewa mata kawai za ta rika yiwa kidan DJ, shi ma saboda ta ji wa'azin malamai ne saboda muhimmancin mace ta zama ita ce ke yiwa mata kida a bukukuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng