Fitaccen Mawaki Kizz Daniel Ya Fadi Alakarsa da Al’ummar Fulani

Fitaccen Mawaki Kizz Daniel Ya Fadi Alakarsa da Al’ummar Fulani

  • Kizz Daniel wanda ya yi shuhura a duniyar mawaka a Najeriya ya sanar wa duniya cewa akwai jinin Fulani a jikinsa
  • Mawakin wanda ya bayyana hakan a shafinsa na X ya ce shi ruwa biyu ne, rabi Fulani rabi Yoruba
  • Bayyana hakan ya biyo bayan wata waka da Kizz ya saki mai suna "Twe Twe" wacce wasu ke ganin cewa ta shafi al'adar Arewacin kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Shahararren mawakin Najeriya, Oluwatobiloba Daniel Anidugbe, wanda aka fi sani da Kizz Daniel, ya bayyana cewa "akwai jinin fulani a jikin na".

Mawakin dan asalin jihar Ogun ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (tsohuwar Twitter) a ranar Talata, 12 ga watan Disamba, 2023.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya bayyana abu 1 tak da zai jawo wa Tinubu faduwa a 2027, ya ba da shawara

Kizz Daniel ya ce yana da tsatso a kabilar Fulani
Shahararren mawakin Najeriya, Kizz Daniel ya ce shi ruwa biyu ne, rabi Fulani rabi Yoruba". Hoto: @KizzDaniel
Asali: Twitter

Kizz Daniel ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A takaice dai ni ruwa biyu ne, rabi Fulani rabi Yoruba,"

Da yawa daga cikin mabiya mawakin sun nuna mamakinsu kan wannan sabon sirrin da ya fitar.

Ga abin da wasu ke cewa:

@easybless3

"Da gaske?"

@ola_bode42

"Idan da gaske ne, ka yi mana waka da Hausa."

@etukudo_jnr

"Ni kaina na yi mamaki"

@SoyoufoundRi

"Kenan kai ba bayerabe ba ne."

@Ladytaeofficial

"A Legas, ba a yi maka kallon bayerabe."

Rahoton Daily Trust ya yi nuni da cewa mawakin ya bayyana hakan ne biyo bayan wata wakarsa mai suna "Twe Twe" da ya saki a kwanan nan.

Mutane da dama na ganin cewa Kizz Daniel ya shigo da al'adun Arewacin Najeriya a wakokinsa, da nufin kara yawan masoyansa daga yankin.

Kizz Daniel ya shahara a 2014 bayan sakin wakar "Woju"

Kara karanta wannan

Mummunan hatsari ya laƙume rayukan aƙalla mutane 10 a babban titi a Najeriya

A shekarar 2013 ne mawakin ya kulla alaka da kamfanin G-Worldwide don yin aiki karkashinsu, amma ya bar kamfanin bayan samun sabani har da zuwa kotu.

A shekarar 2017 ne ya bude nashi kamfanin wakokin mai suna 'Fly Inc', kuma ya yi shuhura a shekarar 2014 bayan sakin wakarsa mai suna "Woju"

Mawakin ya kuma kara yin fice bayan sakin wata wakarsa mai suna "Buga", wacce ta ja hankalin mutanen duniya.

Jaruma Mai Numfashi ta roki yafiyar hukumar tace fina-finan Hausa

A wani labarin, fitacciyar jarumar Kannywood, Khadija Kabir Ahmad, wacce aka fi sani da Khadija Mai Numfashi, ta roki afuwar hukumar tace fina-finai ta jihar Kano.

A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok, Mai Numfashi ta nemi yafiyar hukumar da daukacin jama’ar da bidiyon bai yi wa dadi ba, inda ta ce ita kanta ba ta ji dadin abun da ta aikata a bidiyon ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.