Bidiyon Gida Mai Shekaru 131 da Kakan Matashi ya Gina, Cikinsa Abun Mamaki ne

Bidiyon Gida Mai Shekaru 131 da Kakan Matashi ya Gina, Cikinsa Abun Mamaki ne

  • Wani matashi 'dan Najeriya ya garzaya dandalin TikTok inda ya bayyana bidiyon gidan kakansa wanda aka shekara 131 da ginawa
  • kamar yadda matashin yace, kakaknsa ya gina gidan tun shekarar 1892 kuma har yanzu shekarar 2023 yana tsaye kyam bai rushe ba
  • Bidiyon da ya wallafa ya matukar birge jama'a wadanda suka kalla ginin da idon basira kuma suka ce ya matukar kayatarwa

Wani gida a Najeriya da aka gano an gina shi tun a shekarar 1892 ya bazu a TikTok. Bidiyon gidan an wallafa shi a dandalin inda aka nuna har yanzu yana tsaye kyam a 2023.

Tsohon gida
Bidiyon Gida Mai Shekaru 131 da Kakan Matashi ya Gina, Cikinsa Abun Mamaki ne. Hoto daga TikTok/@itz_promzey.
Asali: UGC

Kamar yadda matashin 'dan Najeriyan ya wallafa bidiyon a shafinsa na TikTok mai suna @itz_promzey, yace kakaknsa ne ya gina wannan shahararren gida.

Bidiyon gidan da aka gina tun 1892

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Daga buya a kwantena, yaro ya farka daga bacci ya tsinci kansa a wata kasa

Lissafi mai sauki da aka yi ya bayyana cewa gidan da aka gina a 1892 yanzu shekarunsa 131.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga cewa gidan na tsaye gyam, gidan ya mallaki wasu fasaloli masu matukar birgewa.

A bayyane yake da kasa a gina gidan kuma har baranda yake da ita da hanyar shiga wacce za ta kai mutum dakuna.

An yi wa gidan rufi da kwanon karfe wanda ake rufi da shi. Abun mamakin shi ne yadda kwanon ya ke kamar sabo.

Har ila yau, akwai wani rami na kiwon kaji tare da kwaryar da ke sagale a daya daga cikin bangon gidan.

Bidiyon babu shakka ya matukar kayatar da jama'a. Kalla bidiyon a kasa:

Martani daga 'yan TikTok

@Irene tace:

"Na ranste yadda wannan gidan ke tsaye gyam da karfinsa yafi wata alakar karfi."

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Matashi Dan Najeriya Ya Dau Zafi, Ya Yi Barazanar Tarwatsa Banki Yayin da Jami’an Tsaro Suka Hana Shi Shiga a Bidiyo

@Twist yayi tsokaci da:

"Su basu cika zakewa kamar mu yanzu."

@Nonye yace:

"Kada mayun kauye su rike ka fa. Soyayya daya 'dan uwa."

@ujunwaprecious61 yace:

"Eyyeh, daga wuri daya muke kuwa."

'Dan Najeriya ya je biki da akwatin kudi, ya dinga watsa sabbi

A wani labari na daban, wani 'dan Najerya da ya je wurin biki da akwatin kudi ya bar jama'a baki bude.

Ya dinga yi wa amarya da nago liki da sabbin bandiran naira da aka canza duk kuwa da wuyar sabbin kudin a kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel