Bidiyon Mai Kama da Buhari ya Karade TikTok Yayin da Yaje Siyan Fetur a Gidan Mai

Bidiyon Mai Kama da Buhari ya Karade TikTok Yayin da Yaje Siyan Fetur a Gidan Mai

  • Wani matashi 'dan Najeriya ya samu nasarar da sai manyan sanannun jama'a ke samu saboda tsabar kamanninsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • A yayin da yayi shiga irin ta shugaban kasan ta kaftani da riga ta leko ta wuyan da hularsa, ya ziyarci gidan mai kuma ya dauka hankalin jama'a
  • Bidiyon wanda ya yadu a soshiyal midiya ya janyo martnai daban-daban na 'yan kasa wadanda suka kasa amincewa ba shugaban kasan bane

Mai tsananin kama da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya janyo cece-kuce bayan ya tsinkayi wani gidan mai cike da salo irin na shugaban kasan.

A bidiyon TikTok din da ke tashe, matashin wanda yayi shiga tsaf irin ta shugaba Buhari ya juya kan jama'a yayin da ya ke tafe hannayensa na lakwashe ta bayansa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Da Yiwuwan A Daina Taron Kamfe, Babban Dan takarar Shugaban Kasa Ya Kamu Da Sabuwar Nauyin Cutar Korona

Mai kama da Buhari
Bidiyon Mai Kama da Buhari ya Karade TikTok Yayin da Yaje Siyan Fetur a Gidan Mai. Hoto daga TikTok/@buhariangus
Asali: UGC

Gajeren bidiyon ya samu sama da masu kallo 440,000 a yayin da ake rubuta wannan rahoto.

Duban da aka yi wa asusun TikTok din mai suna @buhariangus ya nuna cewa an sadaukar da dukkan bidiyoyin da aka wallafa ne don mai kama da Buhari kuma ya na da mabiya 13,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani zai iya sakankancewa matashin yayi amfani da wannan shuhurar inda ya zama mawallafi da bidiyoyin mai kama da Buhari.

Kalla bidiyon a kasa:

'Yan soshiyal midiya sun yi martani

Mosuro Azeez Olanrewaju tace:

"Kai anya da gaske ku ke yi?"

Bossjay yace:

"Buhari: Kai ban san farashin har yanzu da arha ba. Na san abin zan yi. Zan mayar da shi N500 kafin in bar ofis."

Chinaza wisdom Okeke yace:

"Zai fi zama kamar da gaske idan katti majiya karfi biyu na biye da kai."

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Sun Zagaye Mai Kama Da Shugaba Buhari a Wani Bidiyo Da Ya Yadu

Dodo_Ox07 yace:

"Asalin Buharin ba ya iya kai hannunsa baya kamar yadda wannan yayi."

MuhammadMtm yace:

"Matukar ka taba yin soja, toh har abada kai soja ne. Yadda ya tsaya kamar yana filin fareti."

An ga mai kama da Buhari yana tuka motar haya

A wani labari na daban. kwanakin baya an ga wani bawan Allah mai matukar kama da shugaban kasa Muhammadu Buhari yana direban mota a Legas.

Bidiyon bawan Allan ya zagaye intanet inda jama'a suka yi cincirindo suna kallonsa saboda tsabar kama da suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel