Wurinsu Nake Samun Natsuwa: Matar da Biri ya Raina Bayan Anyi Garkuwa da Ita Tana Karama

Wurinsu Nake Samun Natsuwa: Matar da Biri ya Raina Bayan Anyi Garkuwa da Ita Tana Karama

  • Wata tsohuwa ta bayyana yadda birai suka raineta bayan masu garkuwa da mutane sun saceta lokacin tana karama
  • A cewarta, wadanda suka yi garkuwa da ita sun saketa tana gararamba a garin dake makwabtaka dasu, wanda ya cika da birai
  • Matar ta gamsu da rayuwa da birai saboda sun zama masu debe mata kewa kuma da su tayi sabo tun tana karama

Wata tsohuwa cike da alfahari ta bayyana yadda birai suka raine ta bayan masu garkuwa da mutane sun sace ta lokacin da take yarinya.

Tsohuwa mai rayuwa da birai
Wurinsu Nake Samun Natsuwa: Matar da Biri ya Raina Bayan Anyi Garkuwa da Ita Tana Karama. Hoto daga @unilad
Asali: Instagram

A wani bidiyo da @unilad ya wallafa a dandalin Instagram ranar 9 ga watan Janairu, matar ta ce, wadanda suka yi garkuwa da ita sun jefar da ita a tsukuku cike da birai bayan sace ta da suka yi.

Ta kara da bayyana yadda biran daga bisani suka zamo masu debe mata kewa, yayin da suka dauketa hannu bibiyu. Ta koyi yadda za ta nemarwa kanta abinci a dajin bayan kallon yadda biran suke rayuwa.

Kara karanta wannan

"Kullum Yana Zuwa" Bidiyon Alakar Wata Kyakkyawar Malama da Dalibinta a Ofis Ya Bar Mutane Baki Buɗe

Bidiyon ya janyo hankulan dumbun jama'a a kafar sada zumuntar zamani gami da barinsu baki bude saboda tsananin mamaki kan yadda mutum kamarta za ta yarda tayi rayuwa da birai gaba daya rayuwarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zuwa lokacin da aka tattara wannan rahoton, bidiyon ya samu jinjina dubbanni da tsokaci da dama.

Tsokacin jama'a

@lindythea85 ta ce:

"Me ye musabbabin yin garkuwan da farko ma dai? Me mutanen nan za su samu daga wannan."

@samuraumatt300 ya ce:

"Wannan ayabobi ne."

@wookieeeee ya ce:

"Kenan ta bace a dajin tsawon kwanaki ko makwanni, amma duk da haka akwai wani sansanin indiyawa da biran suke aukawa su sace abinci amma bata taba zuwa wurinsu neman agaji ba...? Hakan yayi daidai masoyiya, ke da labarin kanzon kuregenki yayi kama da gaskiya."

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa Tana Rafsar Kuka Bayan ta Debo Ciki, Tana Neman Yadda Za ta Sanarwa Mahaifiyarta

"Ko ki zo ki dauketa ku tafi."

@johnj.rios ya ce:

"Nima na taba hada guba da abinci naci, amma fa a labarin kanzon kurege, wanda yayi kama da naku."

@anandh_.ak._ ya ce:

"Amma me yasa??? Mey e musabbabin garkuwan ma dai?

@zzz_nehra ta ce:

"Wadanda labaran kanzon kuregen sun fara tasiri."

@jock_and_tge_beansprout ya ce:

"Ina ganin ta saba girki sanye da rigar kuku. Nima zan nemi tawa..."

@jhsunell ya ce:

"Tana kokarin bada tatsuniya ne, amma na fara fahimta. Amma an duba wannan batun kuwa?"

@senorxerxes ya ce:

"Na dauki tsawon lokaci a Colombia, kuma wadanda suka iya turanci basu da yawa, ko a babban garin kasuwanci irin Medellín. Ta na nufin birai suka raineta, amma daga bisani ta dawo cikin gari kuma ta saba da rayuwa kamar mutum? Abun dariya."

Bidiyon budurwa tana rangada kuka saboda ta kwaso ciki a waje

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 15 da Aka yi Garkuwa Dasu a Dajikan Zamfara

A wani bidiyo na daban, wata budurwa ta dinga rangada kuka sakamakon cikin da ta kwaso a waje.

Tace bata san yadda za ta sanarwa da mahaifiyarta ba wannan zancen mai bada mamaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel