Mayar Dani Ciki: Jinjiri ya Rike Hannun Likita Bayan an Haife shi, Ya ki Sakinsa a Bidiyo

Mayar Dani Ciki: Jinjiri ya Rike Hannun Likita Bayan an Haife shi, Ya ki Sakinsa a Bidiyo

  • Martani masu ban dariya sun biyo bayan bidiyon wani sabon jinjiri, wanda ya kankame hannun wani likita bayan da aka haife shi
  • Jinjirin yaki sakin hannun likitan inda yayi caraf, inda mutane da dama suka yi wa abun fassra mai ban dariya, duba da abun da jinjirin yayi
  • Duk da irin kokarin da yayi wajen kwatar kansa, jinjirin ya cigaba da kankame hannun likitan kamar bai yi farin ciki da haihuwarsa da aka yi ba

Masu amfani da dandalin Instagram suna ta kokarin fassara bidiyon wani jinjiri da ya kama hannun likita ya kankame.

Jinjiri
Mayar Dani Ciki: Jinjiri ya Rike Hannun Likita Bayan an Haife shi, Ya ki Sakinsa a Bidiyo. Hoto daga Instagram/@BCR Entertainment.
Asali: Instagram

Daga faifan bidiyon, an gano yadda wani sabon jinjiri da ba a dade da haifarsa ba, yayin da likitan ba kai ga cire safar hannunsa ba.m ya rike shi caraf.

Kamar dai bai yi farin cik da zuwansa duniya ba, jinjirin ya kai hannu gami da kankame hannun likitan da karfi.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Dan Siyasa Da Wasu Mutane Uku a Wata Jahar Kudu

Likitan yayi kokarin ganin ya kwaci kansa daga hannun jinjirin, amma hakan bai yuwu ba, saboda jinjirin ya rike yatsansa da karfi gaske.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutane da dama sun yi kokarin fassara manufar jinjirin tare da mamakin dalilin da zai sa ya rike hannun likitan da karfi haka.

Wasu sun tsaya kan cewa jinjirin bai kaunar kasar da likitan ya karba haihuwarsa.

Martanin jama'a

@jibbythekid1 ya ce:

"Yana son komawa."

@shugaplum6454 yayi martani:

"Shin za ka iya fada min dalilin da yasa aka haifo ni a kasar nan?“

@sweetcreature305 ta ce:

" 'Dan karamin jinjirin na son tabbaci."

@,lelcoolj yayi tsokaci:

"Ka mai da ciki!!"

@akpajosephine ta ce:

"A ina nayi gamo da wannan bidiyon mai ban sha'awa... Dubi 'yan kananan hannunshi. Yana son samun tabbaci daga wurin likita."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Dumu-dumu Saurayi Ya Kama Budurwarsa Tana Masa Sata, Tayi Borin Kunya Kiri-kiri

@abdul_hemed_ yayi tsokaci:

”Ke mama ina babana yake ina son tafiya gida fa. Wannan shi ne abun da ya ce a waya."

@sarjosidi ya ce:

"Kamar cewa yayi, babu inda za ka je."

@boseidowu ya ce:

"Eh fa. Babu inda zai je. Dole ya tsaya nan tare dasu."

@abiryuwadialo yayi tsokaci:

"Kalli nan likita, me yasa ka fito da ni? Bari in tabbatar daga Ubangiji idan nan ne inda ya turo ni."

Saurayi ya bukaci Budurwa ta biya kudin zaben baikonsu

A wani labari na daban, wani saurayi ya bukaci budurwarsa da ta biya kudin zoben da ya siya na baikonsu har N2.2 miliyan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel