Kana Da Kyau: Budurwa ‘Yar Najeriya Ta Tunkari Wani Saurayi A Cikin Banki, Ta Karbi Lambar Wayarsa

Kana Da Kyau: Budurwa ‘Yar Najeriya Ta Tunkari Wani Saurayi A Cikin Banki, Ta Karbi Lambar Wayarsa

  • Wata yar Najeriya ta nuna karfin hali inda ta tunkari wani matashi a cikin banki sannan ta nemi ya bata lambar bayansa bayan ta yaba kyawunsa
  • Matashin ya ji dadin yabonsa da budurwar tayi harma ya mika mata hannu suka gaisa yayin da tace tafin hannunsa na da matukar laushi
  • Yan Najeriya da dama sun jinjinawa karfin halin budurwar bayan sun kalli bidiyonta, sai dai wasu sun ce mai yiwuwa mutumin na da aure

Wata budurwa yar Najeriya da ke yin bidiyoyin barkwanci a TikTok ta je shafin intanet don nuna wani bidiyo wanda a ciki ta tsara wani matashi.

A cikin bidiyon, budurwar ta tunkari wani ma’aikacin banki inda ta bayyana masa cewa lallai shi din yana da kyau. Bayan sun sha hannu da shi, sai ta fada masa cewa tafin hannunsa na da matukar laushi.

Kara karanta wannan

Na Fasa: Ana Gab Da Daurin Aure, Ango Yace Ya Fasa Bayan Gano Amaryar Na Da 'Yaya 2

Matashi da budurwa
Kana Da Kyau: Budurwa ‘Yar Najeriya Ta Tunkari Wani Saurayi A Cikin Banki, Ta Karbi Lambar Wayarsa Hoto: TikTok/@philex_cruise_vanshali
Asali: UGC

Mutumin ya karbi wannan yabo da budurwar tayi masa hannu bibbiyu. Bayan ta bar mutumin, sai budurwar ta nuna dan takardar da mutumin ya rubuta masa lambarta a ciki.

Mutane da dama sun yi al’ajabin abun da zai faru idan har ya zamana mutumin na da aure. Yayin da wasu ke da tambayoyi da dama, wasu sun so yadda ta tunkari lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

user8709139382798 ya ce:

“Na fahimta, samun miji ba abu ne mai sauki ba amma ku yarda dani yana da budurwar da zai aura.”

Ta amsa:

“Bana son yin soyayya da shi.”

Sophiat ta ce:

“Duk wadannan yan uwa nawa Musulmi kooo abu nag aba da za ku gani toh hotunan kafin aure ne.”

Ta amsa:

“A’a ba Musulmi bane.”

Ojasope ya ce:

“Ba kya ganin yana da aure idan matarsa ta ga wannan fa.”

Kara karanta wannan

Ba Zan Iya Kusantar Namiji Ba: Kyakkyawar Budurwa Da Aka Nadawa Sarauta Ta Magantu, Bidiyon Ya Janyo Cece-kuce

Uwa Uwace: Bidiyon Nakasasshiyar Uwa Tana Bai wa 'Diyarta Abinci da Bakinta ya Taba Zukata

A wani bidiyo na daban, wata kyakkyawar uwa ta ja hankulan mutane da dama a soshiyal midiya bayan tayi amfani da labban bakinta wajen ciyar da karamar diyarta.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a shafin TikTok, an gano uwar tana diban abinci tare da sakawa karamar diyarta a baki.

Matar mai suna @miminefanmvanyan2 nakasasshiya ce domin dai bata da hannu, a guntule suke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel