2023: Ba Za Mu Zaɓe Ka Ba: Magoya Bayan Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Sun Juya Masa Baya Don Ya Ƙara Aure

2023: Ba Za Mu Zaɓe Ka Ba: Magoya Bayan Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Sun Juya Masa Baya Don Ya Ƙara Aure

  • Fitattun mutane da mabiya sun ci gaba da caccakar Yul Edochie akan yin aure na biyu a sirrance ba tare da sanin matarsa ta fari ba, May Aligwe wacce ya yi shekaru 16 da aurenta
  • Fitaccen jarumin ya bai wa kowa mamaki a ranar Laraba bayan ya bayyana wa duniya hoton jaririn da matarsa ta biyu ta haifa, Judy Austin Muoghalu
  • Tun bayan wallafar ta zagaye ko ina mutane su ke ta caccakar jarumin ta ko ina, har wasu su na ganin kada ya bata lokacinsa wurin takara a 2023, ba za a zabe shi ba

Jama’a su na ci gaba da sukar jarumin kudu, Yul Edochie akan auren sirrin da ya yi da matarsa ta biyu ba tare da sanin matarsa ta farko ba, May Aligwe, wacce su ka yi shekaru 16 da aure.

Kara karanta wannan

Rayuwa tayi wahala: Budurwa yar shekara 70 da ke jiran masoyi na gaskiya ta magantu a bidiyo

Su na da yara 4, maza uku da mace daya.

Karin Aure: Kada Ka Bata Lokacinka Wurin Takarar Shugaban Kasa a 2023, Mutane Ga Yul Edochie
Karin aure: Kada ka bata lokacinka wurin takarar shugaban kasa a 2023, Magoya baya suka fada wa Yul Edochie. Hoto: Vanguard.
Asali: Twitter

A ranar Laraba jarumin ya shayar da kowa mamaki bayan ya wallafa hoton dansa da ya haifa da matarsa ta biyu, Judy Austin Muoghalu, inda kowa ya shaida, rahoton Vanguard.

Tun bayan wallafar ta yadu ne mutane su ke ta sukarsa ta ko ina yayin da wasu su ke shawartarsa da ya hakura da tsayawa takara a 2023 saboda babu wanda zai zabe shi.

Tsokacin mutane karkashin wallafar ta shi

Matarsa ta farko ta nuna rashin jin dadinta inda ta je karkashin wallafar ta rubuta:

“Ubangiji ya yi muku hisabi ku biyu.”

Ganin wannan wallafar ne wata jaruma, Georgina Onuoha ta ce ta rasa abinda za ta ce duk da ta kasance mai magana a bakinta.

Kara karanta wannan

Magidanci ya cika bujensa da iska bayan matarsa ta haifa ƴan huɗu

Sai ta wallafa:

“Komai ya lalace. Kuma yanzu sai tunzura Odogwu ku ke yi. Da za a mayar da lamarin akan matar Agu Nwanyi fah? Za ku yaba mata? Zuciyata ta karye akan wannan lamari.”

Jaruma Joyce Kalu ta ce:

“Lallai rayuwar nan sai a hankali.”

Jaruma Shan George ta nuna mamakinta akan lamarin inda ta ce:

“Tsaya Yul, dagaske ka ke? Wannan abin ya ba ni mamaki. Bari dai in ci abinci tukunna....”

Fitacciyar mawallafiya Blessing kuwa yaba wa Yul ta yi akan yadda ya bayyana laifinsa inda ta yi wata wallafa a Instagram ta na cewa:

“Ina girmama mazan da su ke tafka laifi kuma su amsa shi. Ina ganin girman Yul Edochie. Yadda ya tsaya akan laifinsa ya birge ni.”

Na yi murabus daga ɗirka wa 'yan mata ciki, Mawaƙi 2Baba

A wani labarin, Shaharraen mawakin Najeriya da ya lashe kyaututuka da dama, Innocent Idibia da aka fi sani da 2Baba ya bayyana cewa ba zai sake yi wa wata mace ciki ba, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga Fara Magana a Facebook: Baturiya Ta Baro Amurka Ta Yi Wuff Da Wani Matashi a Najeriya, Hotunansu Ya Ɗauki Hankula

Mawakin, da ya yi wakar 'African Queen' ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta yayin bikin al'adu da kadade ta Idoma International Carnivial da aka yi a Otukpo, garinsu su 2Baba a Jihar Benue.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164