Kannywood: An Taɓa Ɗaure Min Hannu Aka Jefa Ni Cikin Rafi Saura Ƙiris Kada Ya Yi Kalace Da Ni, Baba Musa

Kannywood: An Taɓa Ɗaure Min Hannu Aka Jefa Ni Cikin Rafi Saura Ƙiris Kada Ya Yi Kalace Da Ni, Baba Musa

  • Jarumin fina-fina, Musa Muhammad Abdullahi da aka fi sani da Baba Musa a 'Kwana Casa'in' ya bayyana cewa rashin hadin kai ne babban kalubalen da ke damun Kannywood
  • Baba Musa cikin wata tattaunawa da aka yi da shi ya magantu kan abin da ba zai taba mantawa inda ya ce an taba jefa shi cikin rafi a daure kuma kada ta nufo inda ya ke
  • Tsohon Jarumin Fina-Finan ya kuma ce akwai banbanci tsakanin jaruman yanzu da na zamaninsu amma yana da yakinin cewa za a samu cigaba a masana'antar

Musa Muhammad Abdullahi, da aka fi sani da Baba Musa, tsohon jarumi ne da ya fara fitowa a fina-finai tun kafin a kafa Kannywood kuma a yanzu yana cikin taurarin dirama mai dogon zango mai suna 'Kwana Casa'in.'

Kara karanta wannan

Amaechi: Dama na yi hasashen za a kawo hari a jirgi, na nemi kayan tsaro amma aka hana

A hirar da Daily Trust ta yi da shi, ya yi magana kan batutuwa da dama da suka shafi karatunsa, aikinsa, masana'antar fim na Kano da Kaduna, sauye-sauye da aka samu da kallubalen da ake fuskantar ds.

Kannywood: An Taɓa Ɗaure Min Hannu Aka Jefa Ni Cikin Rafi Saura Ƙiris Kada Ya Yi Kalace Da Ni, Baba Musa
Musa Muhammad Abdullahi, da aka fi sani da Baba Musa. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

An masa tambaya kan kallubale mafi girma da ya taba fuskanta kawo yanzu, kuma ya kada baki ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na ga abubuwa da dama a harkar fim. Akwai fim din da muka yi inda wasu mata suke amfani da hijabi wurin aikata abu mara kyau. A lokacin, akwai tsatsaurin ra'ayin addini. Wasu masu tsaurin ra'ayin suka ce dukkanmu jaruman a halaka mu.
"Wata rana ina tafiya a Tundun Wada Kaduna, wani cikin matasan ya gane ni ya sanar da sauran, suka taho da nufin kai min hari. Amma na yi sa'a wasu matasa suka kare ni kuma yan sanda suka kama su.

Kara karanta wannan

Kazantar da baka gani ba: Bidiyon yadda wani ke buga ruwan roba da hannu ya girgiza intanet

"Akwai kuma wani abin da ba zan taba mantawa ba lokacin muna yi wa TV Kaduna wani shiri mai suna Telefest. A cikin wani shirin da na fito a matsayin dan siyasa, yan daba sun jefa ni cikin Rafin Kaduna.
"Bayan sun daure hannu na sun jefa ni cikin rafin, na hangi kada yana zuwa daga nesa, mai shirya wasan, marigayi Umar Hassan, shima ya hangi kadan na zuwa kuma cikin gaggawa ya umurci a ceto ni. Ni tsira ba rauni. Na gode wa Allah bisa kyautar rayuwa."

Bugu da kari, Baba Musa kamar yadda Daily Trust ta rahoto ya ce yana ganin za a samu cigaba da alheri a masana'antar na Kannywood ya kuma yi kira ga jaruman su hada kansu wuri guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164