Hotunan Budurwar Da Ta Ce Saurayinta Ya Rabu Da Ita Saboda Tsawonta Sun Bazu a Dandalin Sada Zumunta

Hotunan Budurwar Da Ta Ce Saurayinta Ya Rabu Da Ita Saboda Tsawonta Sun Bazu a Dandalin Sada Zumunta

  • Wata doguwar budurwa ta sha caccaka a kafafen sada zumunta bayan ta wallafa hotonta cike da alfahari da surarta
  • A cewarta, saurayinta da suke ta soyayya da shi tsawon lokaci ya rabu da ita ne saboda tsayin kafafunta, ba sa burge shi
  • Ta wallafa hotunanta inda ta bayyana yadda ta yanke shawarar fara tallar tufafi maimakon ta zauna tana alhinin gudunta da ya yi

Wata matashiyar budurwa ta janyo surutai a kafafen sada zumunta bayan ta wallafa hotunan dogayen kafafunta.

A wani hoto da shafin yabaleftonline na Instagram ya wallafa, budurwar ta ce saurayinta ya rabu da ita ne saboda dogayen kafafunta.

Hotunan Budurwar Da Ta Ce Saurayinta Ya Rabu Da Ita Saboda Tsawonta Sun Bazu a Dandalin Sada Zumunta
Hotunan Budurwar Da Ta Ce Saurayinta Ya Rabu Da Ita Saboda Tsawonta Sun Bazu a Soshiyal Midiya. Hoto: @yabaleftonline.
Asali: Instagram

Kara karanta wannan

Zukekiyar budurwa na shirin siyar da motarta don daukar nauyin karatun saurayinta

Sakamakon yadda soyayya ta ki amsarta, budurwar ta ce za ta koma tallar sutturu. Ta wallafa bidiyonta tana gwada tafiya irin ta masu tallace-tallacen.

Nan da nan mutane suka yi caa suna tsokaci karkashin bidiyon da kuma hotunan, har wasu suna musanta maganarta wanda ta ce kafafun nata suna ganin kamar kawai a hoto ne.

Ga bidiyo a kasa:

Ga wasu daga cikin tsokacin mutane

thethilda ta ce:

“Duk da tsayinta ta burgeni da take sanya dogayen takalma. Tsayina sawu 5 da inci 11 ne kuma ina ganin kamar tsayina ya yi yawa shiyasa nake sanya takalma marasa tsayi.”

mili_vibez ta ce:

“Da ni nake da wadannan dogayen kafafun, da bazan zauna a Najeriya ba, kasar Canada zan tsere.”

som_miles ya ce:

“Da can bai san kina da dogayen kafafun ba ne ko kuma boye mishi su ki ka yi? Sai ku dinga wallafa shirme..”

Kara karanta wannan

Daga kwana a jikin Saurayinta da suka haɗu a Facebook, wata kyakkyawar budurwa ta zama Bebiya

healanseesaghost ta ce:

“Idan saboda dogayen kafafunta ya rabu da ita, me yasa tun farko yafara soyayya da ita? Ba fa kawai bayyana suka yi ba.”

Ba zan iya ba: Jarabar mijina ta yi yawa, yana so ya kashe ni da saduwa, Matar aure ga kotu

A wani labarin, wata matar aure mai 'ya'ya uku, Olamide Lawal, a ranar Juma'a ta roki kotun Kwastamare da ke zamansa a Mapo, Ibadan, ya raba aure tsakaninta da mijinta, Saheed Lawal, saboda yana jarabar ta da yawan saduwa, rahoton Premium Times.

A karar da ta shigar, Olamide wacce ke zaune a Ibadan ta kuma yi ikirarin cewa mijinta ya saba shan giya ya yi tatil yana maye, The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel