Zukekiyar budurwa na shirin siyar da motarta don daukar nauyin karatun saurayinta

Zukekiyar budurwa na shirin siyar da motarta don daukar nauyin karatun saurayinta

  • Wata budurwa da ta sha alwashin daukar nauyin saurayinta ya yi digiri na biyu ta sha martani
  • Kamar yadda budurwar ta ce, ta fahimci cewa maza suna bautawa macen da suke so, hakan yasa take son kwatanta nata
  • Jama'a sun dinga mata martani bayan ta sanar da shirinta inda wasu ke cewa za ta yi kukan jini a nan gaba kadan

Wata budurwa ta janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan ta ce za ta siyar da motar ta domin daukar nauyin digiri na biyu na saurayinta.

Kyakyawar budurwar ta kara da cewa, za ta yi amfani da ragowar kudin wurin fara kasuwanci saboda saurayinta wanda ya cancanci kyautatawa.

Zukekiyar budurwa na shirin siyar da motarta don daukar nauyin karatun saurayinta
Zukekiyar budurwa na shirin siyar da motarta don daukar nauyin karatun saurayinta . Hoto daga Joy Turamuhawe
Asali: UGC

"Ina son siyar da mota ta domin daukar nauyin saurayina wurin yin digiri na biyu," Joy Turamuhawe tace.

Kara karanta wannan

Badakalar kwalin NYSC: Kullun sai na yi kuka har tsawon watanni uku, Tsohuwar ministar Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata tattaunawa da ta yi da Tuko.co.ke, Turamuhawe ta ce ta yarda da mayar da alheri da alheri.

"Ina ganin yadda maza ke kyautatawa Matan da suke so kuma ni na yarda da saka alheri da alheri," Turamuhawe ta ce.

A yayin da ta wallafa labarinta a Twitter, jama'a sun yi caa a kanta inda suka dinga martani.

Joansheenah tace: "Babu shakka za a yi nadama, ki tambaye ni ina wacce ta siyawa saurayin PS."
Broke _celebrity cewa tayi: "Idan wannan gaskiya ne, ina son zama saurayin ki. Ina nan ina tambayar yadda mutum ke neman digiri na biyu kuma bashi da aikin yi."
Marvin K: "A gaskiya kada ki siyar da motar ki. Idan zai yuwu, ki samu bashi sai ki yi amfani da motar ki a matsayin jingina daga nan sai ki biya a hankali. Za ki iya bukatar motar ki kuma saurayin ki ya yi sa'a."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Bidiyon yadda mata ta shekara tana tara kudi a asusu, ta ga N90 yagaggu

The Chemist cewa yayi: "A gaskiya ban amince da matsayar Rose ba, samun bashin da za ka biya da ruwa tare da ajiye mota bashi da amfani."

Ta tabbata: Budurwar da ta yi wa Jaruma mai Kayan Mata kwacen miji, ta bayyana

Fitacciyar mai siyar da kayan mata, Hauwa Saidu wacce aka fi sani da Jaruma, ta zama abun zunde da yafice bayan wata budurwa ta kwace mata mijinta.

Soshiyal midiya ta cika da labarin bayan sabuwar budurwar Ross Fahad Isabor, tsohon mijin Jaruma mai suna Jasmine London, ta bayyana kanta.

Sau da yawa Jaruma kan bugi kirji tana fadin cewa ta san duk hanyoyin mallake miji ballantana da taimakon Kayan Mata da take siyarwa. Wannan lamarin ne yasa jama'a masu yawa suka sha mamakin yadda budurwar ta kwace mata miji cike da nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel