Dalilin Gwamnan Borno na Goyon Bayan Harin Sojin Sama duk da Rasa Rayuka akalla 200

Dalilin Gwamnan Borno na Goyon Bayan Harin Sojin Sama duk da Rasa Rayuka akalla 200

  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi cikakken bayani game da kasuwar da sojojin sama suka jefa wa bama-bamai a ƙarshen mako
  • A cewar Farfesa Zulum, an riga an rufe kasuwar Jilli shekaru biyar da suka wuce saboda an gano ta zama dandalin ƴan ta'adda
  • Gwamnan ya goyi bayan aikin sojojin tare da gargaɗin mazauna jihar Borno a kan mu'amala da ƴan ta'adda saboda kare rayukansu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayyana cewa kasuwar Jilli da ke karamar hukumar Gubio, inda aka kai harin sama da ya haddasa asarar rayuka, an rufe ta shekaru biyar da suka gabata.

Ya bayyana hakan ne bayan rahotanni sun bayyana cewa dararen hula akalla 50 ne ake fargabar sun rasu sakamakon harin sojin saman Najeriya.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi kuskuren kai hari, sun kashe fararen hula kusan 200 a Borno

Gwamnan Borno ya ce an rufe kasuwar da sojojin suka kai wa hari tuntuni
Gwamnan Borno yana jawabi a Borno Hoto: The Governor of Borno state
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa sai dai gwamnan ya ƙare aikin sojojin a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Dauda Iliya, ya fitar a ranar Lahadi, 12 ga watan Afrilu, 2026.

Gwamnan Borno ya ƙare ayyukan sojoji

Channels TV ta wallafa cewa kasuwar Jilli ta dade tana zama wata cibiyar da ake zargin ‘yan ta’adda da masu kai kai masu kayan aiki suna amfani da ita wajen cinikayya.

Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce ya samu cikakken bayani kan harin da rundunar sojin sama ta Operation Hadin Kai ta kai a yankin.

Ya jaddada cewa gwamnatin jihar Borno ta dauki matakin rufe kasuwannin Jilli da Gazabure tun shekaru biyar da suka wuce domin dakile ayyukan ta’addanci da suka addabi yankin.

Ya kuma kara da cewa yana tattaunawa da gwamnatin jihar Yobe da manyan hafsoshin soji domin fahimtar lamarin da kuma daukar matakan da suka dace.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashin ɗan majalisa daga Kano, Hon Danjuma ya rasu

Gargaɗin Gwamnan jihar Borno ga jama'a

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin sa na aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro kafin a sake bude kasuwanni ko a mayar da mutane yankunan da rikicin ya shafa.

Sojojin sama sun kai hari Jilli
Jiragen sojin saman Najeriya a yayin kai wani hari kan ƴan ta'adda Hoto: Nigerian Airforce HQ
Source: Twitter

Wannan, a cewarsa, na daga cikin matakan tabbatar da tsaro da kare rayukan jama’a daga miyagun ƴan ta'adda a yankin.

Ya yi gargaɗin cewa bai dace jama'a su rika taimaka wa ƴan tayar da kayar baya ta kowacce fuska a yankin ba, don haka ne za a iya kare rayukansu.

Haka kuma, gwamnan ya bukaci al’umma da su kasance masu lura da kuma bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gudanar da ayyukan tsaro yadda ya kamata.

Sojoji sun yi kuskuren kai hari Borno

A baya, kun ji cewa jirgin yaƙin sojojin saman Najeriya ya saki wuta a kasuwar mako-mako ta Jilli da ke iyakar Borno da Yobe, akalla mutane 200 suka riga mu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

Sunayen manyan jami'an sojin Najeriya da suka mutu a bakin aiki daga 2016 zuwa 2026

Jiragen yaƙin suna bin sawun wasu ƴan ta'adda ne da suka zo karɓar haraji, sai dai an samu kuskure, inda harin ya faɗa kan talakawa ƴan kasuwar Jilli.

Shugabannin yankin sun tabbatar da cewa an kwantar da mutane da dama a asibitin ƙwararru na Geidam, wasu kuma an tura su Damaturu domin samun kula wa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng