'Sun Aikata Zunubi': Gwamnatin Tarayya Ta Tura Mutane 386 Gidan Yari a Abuja
- Gwamnatin Tarayya ta kammala shari'ar mutane 508 da ake zargi da ta'addanci, inda aka samu nasarar yanke wa mutane 386 hukunci
- Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi, ya bayyana cewa an saki mutane 8, an wanke wasu 2, sannan an ɗage shari'ar mutane 112 zuwa wani lokaci
- Lateef Fagbemi ya ce za a gudanar da kashi na 10 na wannan shari'a ta bai-ɗaya tsakanin ranakun 15 zuwa 18 na watan Yunin 2026
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutane 386 hukuncin zama a gidan yari daga cikin mutane 508 da aka gurfanar kan laifuffukan ta'addanci.
Babban lauyan gwamnati kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala kashi na tara na shari’ar 'yan ta'addar da aka gudanar a cikin mako guda.

Source: Twitter
Kotu ta daure mutane 386 a gidan yari
Fagbemi ya bayyana gamsuwarsa da yadda shari’ar ta gudana cikin gaskiya da bin doka, kamar yadda rahoton Punch ya nuna.
A cewar ministan, daga cikin mutane 508 da aka kawo gaban kotun, mutane takwas aka sallama, yayin da aka wanke mutane biyu baki ɗaya. Sauran mutane 112 kuma an ɗage shari’arsu zuwa kashi na gaba na zaman kotun.
Fagbemi ya jaddada cewa sallama da wanke wasu da aka yi na nuna cewa gwamnati tana bin tsarin shari'a yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa:
"Alama ce ta riko da gaskiya yadda har kotu ta saki wasu kuma aka wanke wasu, hakan ya nuna cewa muna bin matakan shari’a yadda ya kamata. Duk wanda ba shi da laifi ba za a tura shi gidan yari ba."
Shirye-shiryen shari'a ta 10
Shari’ar, wadda aka fara a ranar Talata, 7 ga Afrilu, 2026, ta gudana ne a gaban alkalai 10 na Babbar Kotun Tarayya duk da hutu na bikin Easter da aka fara a ranar.

Kara karanta wannan
An yanke wa ɗan takarar sanata hukuncin ɗaurin shekaru 10 kan alaka da Boko Haram
Ministan ya bayyana cewa an riga an tsara lokacin da za a ci gaba da shari’ar ga sauran waɗanda ake zargi.
"Wannan shi ne kashi na tara. Kashi na goma zai gudana tsakanin ranar 15 zuwa 18 na watan Yuni, idan Allah ya kaimu," in ji Fagbemi.
Ya ƙara da cewa waɗannan hukunce-hukunce da kotu ta yanke za su zama darasi ga masu tallafa wa ta'addanci da kuma masu ƙoƙarin tayar da ƙayar baya a Najeriya.

Source: UGC
Kungiyoyin da suka halarci zaman kotu
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa an yanke wa wadanda aka samu da laifi hukuncin zaman gidan yari daban-daban, kama daga shekara takwas har zuwa daurin rai-da-rai.
Domin tabbatar da adalci da gaskiya, kungiyoyi da dama sun halarci zaman kotun a matsayin masu sanya ido, ciki har da kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), hukumar kare hakkin dan-adam ta kasa, Kungiyar Amnesty International, Da wasu kungiyoyin farar hula.
An saki sunayen masu daukar nauyin ta'addanci
Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Tarayya ta sabunta jerin sunayen mutane da ƙungiyoyi 48 da aka ayyana a matsayin wadanda ke daukar nauyin ta'addanci.

Kara karanta wannan
'Za mu ci gaba da kai hari,' Isra'ila ta sake tsokano Iran da ta kashe mutane a Lebanon
An dauki wannan matakin ne da nufin toshe hanyoyin samun kuɗaɗe, kadarori, da duk wani tallafi da ke taimaka wa masu tada ƙayar baya.
Jerin sunayen ya haɗa da fitattun ƙungiyoyi irin su ISWAP, Ansaru, da IPOB, tare da mutane irin su Tukur Mamu, Fatima Ishaq da sauran su.
Asali: Legit.ng
