Tsohon Ɗan Majalisa Ya Ƙare Kansa kan Zargin Fitar da bayan Sirrin Najeriya ga Ƙasashen waje
- Tsohon ɗan majalisa kuma ƙwararren masani kan harkokin tsaro, Aliyu Ibrahim Gebi ya musanta zargin da ake yi masa a kan tsaron Najeriya
- Rahotanni sun bayyana cewa Gebi ya bayar da bayanan sirri na ƙarya ga ƙasashen waje har ya razana su sosai
- Aliyu Ibrahim Gebi ya ce duk ayyukansa sun ta’allaka ne kan kishin ƙasa da kare muradun Najeriya ba wai yaɗa labaran ƙarya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon ɗan majalisa kuma ƙwararren masani kan harkokin tsaro, Aliyu Ibrahim Gebi, ya musanta zarge-zargen da ke alaƙanta shi da bayar da bayanan sirri na ƙarya ga ofisoshin jakadancin ƙasashen waje.
Gebi ya bayyana cewa ba zai taɓa furta wani abu mara kyau game da Najeriya ba, ko shugabanta, ko shugabannin hukumomin tsaro ba.

Source: Twitter
Zagazola Malama ya wallafa a shafin X cewa tsohon ɗan majalisar ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a 10 ga watan Afrilu, 2026.
Tsohon ɗan majalisa ya ƙare kansa
Premium Times ta wallafa cewa Gebi ya ce kokarin karkatar da gudunmawar da ya bayar zuwa wani mummunan abin takaici ne kuma ba daidai ba ne da tarihinsa a hidimar ƙasa.
Gebi ya yi tambaya kan tushen rahotannin da ke cewa bayanan sirrin da ake danganta masa sun yi tasiri ga gargadin tafiye-tafiye daga ƙasashen waje da kuma matakan diflomasiyya da suka shafi martabar Najeriya a duniya.
A cewarsa, bai dace a jingina irin waɗannan manyan hukunci ga abu guda kawai ba, yana mai cewa irin wannan fahimta ba dai-dai ba ne.
Ya jaddada cewa ya taba taka muhimmiyar rawa a lokutan baya wajen kare martabar ƙasar, musamman a zamanin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, lokacin da aka fara maganar yiwuwar fitar da jami’an diflomasiyya na ƙasashen waje daga Najeriya.
Tsohon ɗan majalisa ya ba da shawara
Gebi ya kuma yi tsokaci kan sauye-sauyen da ake samu a harkokin tsaro na duniya, yana mai cewa dole ne a duba alaƙar ƙasashen waje da Najeriya a mahangar sababbin tsare-tsaren musayar bayanan sirri.
Ya gargadi cewa ya kamata a yi taka-tsan-tsan sosai wajen tafiyar da bayanan sirri, domin guje wa yanke hukunci cikin gaggawa wanda zai iya lalata amana tsakanin mutane, hukumomi da kuma ƙasashen duniya.

Source: Facebook
Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa ga hukumomin tsaron Najeriya kamar ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, DSS da rundunar sojoji, yana mai cewa suna samun ci gaba wajen magance matsalolin tsaro.
Gebi ya bukaci masu ruwa da tsaki su guji daukar matakai bisa fushi ko siyasa, su rungumi bin doka da oda wajen magance irin waɗannan batutuwa.
Ya ce:
“Bai kamata mu jefar da jariri tare da ruwan wanka ba."
Ya bayyana kansa a matsayin ɗan kishin ƙasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga Najeriya, yana mai cewa:

Kara karanta wannan
DSS ta gano tsohon 'dan majalisa da ya kada hantar Amurka da rashin tsaro a Najeriya
"Ina son ƙasata. Na zubar da jini domin ƙasata. Kuma ba zan daina kare ta ba.”
DSS na binciken tsohon ɗan majalisa
A baya, mun wallafa cewa jami’an tsaro sun kama tsohon ɗan majalisar tarayya, Aliyu Gebi, bisa zargin bayar da rahoton tsaro na ƙarya ga ofisoshin jakadanci.
Rahoton da ake zargin ya haddasa tashin hankali har wasu kamfanonin jiragen sama suka soke zirga-zirga zuwa Najeriya saboda bayanan da suka samu.
Ana ci gaba da bincike duk da cewa an bayar da belinsa, ana kuma shirin gurfanar da shi a kotu domin bibiyar batun kamar yadda doka ta tanada.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

