Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kutsa cikin Otal, Sun Sace Shugaban Karamar Hukuma a Najeriya
- Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Sapele, Hon. Bright Abeke da ke jihar Delta
- Rahotanni sun nuna cewa an girke jami'an tsaro a duk wata hanyar shiga da ta fita Sepele da nufin ceto ciyaman din cikin koshin lafiya
- Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan, wadanda yawansu ya kai kusan 15, sun afka cikin wani otal, suka tafi da Hon. Abeke
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Delta, Nigeria - Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta sun katange manyan hanyoyin shiga da fita na garin Sapele da ke Karamar Hukumar Sapele da shingayen bincike.
Dakarun 'yan sandan sun dauki wannan matakin ne biyo bayan sace shugaban karamar hukumar Sapele, Hon. Bright Abeke da wasu mahara da ba a sani ba suka yi.

Source: Original
'Yan bindiga sun sace ciyaman a Delta

Kara karanta wannan
Abin tausayi: An shiga firgici da aka gano gawarwakin mutane sama da 60 a jihar Neja
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an yi awon gaba da Hon. Abeke ne da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Juma’a a wani otal da ke kan titin Owumi a Sapele.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar sun yi nasarar tafiya da shugaban karamar hukumar ne bayan sun yi musayar wuta da jami'an tsaronsa.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan, wadanda yawansu ya kai kusan 15, sun afka cikin otal din inda suka nufi dakin shugaban karamar hukumar kai-tsaye kafin su yi awon gaba da shi.
Yadda maharan suka kutsa kai otal
An ce maharan sun zo ne a cikin wata motar alfarma samfurin Range Rover da wasu motoci guda biyu, inda suka rika harbi a iska domin tarwatsa baki da masu kallo.
'Yan bindigar sun harbi wani mamba na kungiyar 'yan sa-kai ta yankin, wanda aka gano jami'in rundunar Ufuoma ne ta hanyar kayan kungiyar da ke jikinsa.
Bayanai sun nuna cewa maharan suka dauke shi a matsayin barazana, inda suka harbe shi yayin farmakin, aka garzaya da shi asibiti mafi kusa domin yi masa magani.
“Masu garkuwan na dauke da makamai, kuma sun nuna rashin tsoro, sun ajiye motocinsu a wurare daban-daban a kewayen otal din, suna ta harbe-harbe don korar mutane da baki,” in ji wani shaidun gani da ido.

Source: Getty Images
Matakan da jami'an tsaro suka dauka
A halin da ake ciki, wata majiyar ‘yan sanda wadda ta tabbatar da cewa ana kokarin ceto shugaban da aka sace, ba ta iya tabbatar da halin da dan bangar da aka raunata ke ciki, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
“An kafa shingen bincike a manyan hanyoyin shiga da fita na Sapele. Za mu kamo su kuma mu ceto ciyaman cikin koshin lafiya," in ji majiyar.
'Yan bindiga sun kai farmaki coci a Ondo
A wani rahoton, kun ji cewa wasu ’yan bindiga sun kai farmaki Cocin Celestial Church of Christ (CCC) da ke garin Uso, a karamar hukumar Owo ta Jihar Ondo.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yan ta'addan sun kai wannan hari ne da safiyar Laraba da ta gabata, inda suka yi awon gaba da masu ibada shida.lokacin da ake gudanar da taron addu'o'i.
Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi domin tarwatsa mutane kafin su yi awon gaba da masu ibada.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
