Nasara daga Allah: 'Yan Bindiga Sun Gamu da Ajali, Sama da 100 Sun Sheka Lahira

Nasara daga Allah: 'Yan Bindiga Sun Gamu da Ajali, Sama da 100 Sun Sheka Lahira

  • 'Yan bindiga fiye da 100 sun sheka barzahu a musayar wuta da jami'an tsaro a kauyukan karamar hukumar Shiroro na jihar Neja
  • Kwamishinan yada labarai na jihar Neja, Nuhu Nana ya bayyana cewa yayin artabun, an rasa 'yan banga 14 da fararen hula biyu
  • Gwamnatin Neja ta tabbatar wa jama'a aniyarta na kare rayuka da dukiyoyi, inda ta bayyana cewa an tura karin jami'ai da sababbin dabaru

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - An tabbatar da mutuwar 'yan banga 14, ciki har da kwamandan su na Bagna da ke Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja, da kuma fararen hula guda biyu.

Lamarin ya faru ne sakamakon wani sabon hari da 'yan bindiga suka kai kauyukan Bagna da Yelwa a yankin karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: An shiga firgici da aka gano gawarwakin mutane sama da 60 a jihar Neja

Gwamna Bago.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago a gidan gwamnatinsa da ke Minna Hoto: Hon. Bago
Source: Twitter

Gwamnatin Neja ta mika sakon ta'aziyya

Kwamishinan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na jihar, Nuhu Nana, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, in ji rahoton Channels tv.

Gwamnatin Neja ta yi juyayi kan asarar rayukan da aka samu a yayin ayyukan tsaro, kuma ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamatan, tare da jinjina wa jajircewarsu da sadaukarwar da suka yi a yakin da ake yi da rashin tsaro.

An kashe 'yan bindiga 110 a jihar Neja

A gefe guda kuma, an ba da rahoton kashe jimillar ‘yan bindiga 110 a wurare daban-daban a Shiroro, a matsayin wata babbar nasara ta tsaro da aka samu a jihar Neja.

Bayanai sun nuna cewa an kashe 'yan bindiga 47 a kauyen Lantan, 21 a Lakupe, 16 a Luwidna, 20 a Farin Kasa da kuma 6 a Rafin Barden Dawaki, cewar Premium Times.

Hakan na zuwa ne yayin da Gwamnatin Jihar Neja ta sake nanata aniyarta na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Shiroro biyo bayan hare-haren 'yan fashin.

Kara karanta wannan

Za a jika wa APC aiki, tsohon jagoran yakin neman zaben Tinubu a Zamfara ya koma ADC

Gwamnatin Neja ta sake zage dantse

Gwamnatin ta bayyana cewa sakamakon wannan nasara ya nuna tasiri da kuma juriya na hadin gwiwar jami'an tsaro da nufin ruguza miyagu da maido da zaman lafiya a kauyukan da abin ya shafa.

Yayin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa, gwamnatin ta shawarci mazauna yankin da su kasance cikin shiri, su guji zirga-zirgar da ba ta da muhimmanci a wuraren da ke da hadari, sannan su ba wa jami’an tsaro cikakken hadin kai.

Sojoji.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya yayin da suke bakin aiki Hoto: @NigerianArmy
Source: Twitter

Gwamnatin Neja ta tabbatar wa jama'a aniyarta na kare rayuka da dukiyoyi, inda ta bayyana cewa an tura karin jami'ai da sababbin dabaru domin dorewar wannan nasara da kuma hana afkuwar wasu hare-haren.

An gano gawarwakin mutane 61 a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa ana ci gaba da samun bayanai daga mummunan harin da yan bindiga suka kai yankin karamar hukumar Shiroro a Neja ranar Talata da ta wuce.

An gano aƙalla gawarwaki 61 na jami’an tsaro da fararen hula da aka kashe a harin ‘yan bindiga da aka kai Naje, lamarin da ya firgita mazaunaa yankin musamman mata da yara.

Mazauna yankin sun ce an kwaso gawarwakin ne a dazukan da ke kusa kwanaki kadan bayan harin yan bindigar, inda aka birne fararen hula a garin Erena.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262