Tinubu na Tattaunawa da Amurka da Wasu Kasashen Waje kan Tsaron Najeriya

Tinubu na Tattaunawa da Amurka da Wasu Kasashen Waje kan Tsaron Najeriya

  • Jakadan Najeriya a majalisar dinkin duniya ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu na tattaunawa da kasashe domin nemo mafita ga matsalolin tsaro
  • Jimoh Ibrahim ya bayyana cewa Najeriya ba ta dogara da kasa guda wajen magance matsalolin tsaro ba, yana mai cewa ana maraba da agaji daga kasashe
  • A bayanin da ya yi a Amurka, ya jaddada cewa Najeriya kasa ce mai cikakken iko da za ta cigaba da zama daya duk da kalubalen da ta ke fama da su

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Jakadan Najeriya a majalisar dinkin duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na tattaunawa da kasashe kan matsalar tsaro.

Ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a New York yayin da ya isa domin fara aikinsa a matsayin sabon jakadan Najeriya, inda ya tabbatar da cewa Tinubu zai magance matsalolin tsaron kasar.

Kara karanta wannan

Tsadar man fetur: Tinubu ya nuna kukan dadi 'yan Najeriya ke yi

Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu yayin wani jawabi a Katsina a 2025. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Kasashen da Tinubu ke magana da su

Vanguard ta wallafa cewa Jimoh Ibrahim ya ce Najeriya ba ta takaita kan wata kasa guda ba, yana mai cewa duk wata kasa da ke da mafita ga matsalolin tsaron Najeriya ana tuntubar ta.

Ya ce:

“Najeriya kasarmu ce. Za mu iya samun matsaloli kamar Boko Haram amma mun shiga hulda da kasashe da dama domin magance su,”
“Ba mu dogara da kasa daya tilo ta zo ta taimaka mana ba. Muna neman kasashe da dama su zo su taimaka mana.
“Kamar yadda Amurka ke nan, Shugaban kasa na tattaunawa da Istanbul (Turkiyya), kuma ba mu dade da tattaunawa da Landan (Birtaniya) ba.
“Yayin da muke tuntubar masu ruwa da tsaki, muna maraba da duk wanda ke son taimaka mana warware matsalolinmu, kuma muna girmama su sosai.”

Ya jaddada cewa kowace kasa a duniya ta taba fuskantar kalubale a wani lokaci, inda ya kawo misali da harin ta’addanci na ranar 11 ga Satumba a Amurka.

Kara karanta wannan

'Ku kwantar da hankulanku': Martanin Najeriya bayan gargadin Amurka a Abuja

Jimoh Ibrahim da Bola Tinubu
Jimoh Ibrahim tare da shugaba Bola Tinubu a Abuja. Hoto: Jimoh Ibrahim
Source: Facebook

Najeriya za ta hada kai da kasashe

A cewar Jimoh Ibrahim, Tinubu ne ya aike shi Majalisar Dinkin Duniya domin hada kan al’ummar duniya wajen taimakawa Najeriya.

Tsohon sanatan da ya wakilci Ondo kafin tura shi jakadanci, ya jaddada cewa Najeriya kasa daya ce mai cikakken iko da ba za a raba ta ba.

Punch ta rahoto ya ce:

“Shugaban kasa zai yi nasara. Dole Najeriya ta kasance kasa daya mai cikakken iko,”
“Abin da aka aiko ni na yi a nan shi ne tabbatar da cewa Najeriya kasa daya ce da ba za a raba ta ba – ba za a fara maganar rabuwarta ba ma.

Tinubu ya magantu kan tsadar mai

A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan tsadar fetur da ake fama da shi a duniya.

Ya bayyana cewa tsadar ta samo asali ne daga yakin da aka yi tsakanin Amurka/Isra'ila da Iran kuma ta shafi kasashe da dama.

Tinubu ya yi nuni da cewa an fi tsadar fetur kasar Kenya da wasu kasashen Afrika a kan Najeriya, amma duk da haka zai cigaba da kokari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng