Tsadar Man fetur: Tinubu Ya Nuna Kukan Dadi 'Yan Najeriya ke Yi
- Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya fito ya yi magana kan tsadar man fetur da ake fama da shi a kasar nan a wani taro a Bayelsa
- Tinubu ya ce jama'a na fama da wahalar rayuwa, amma a cewarsa, dan Najeriya kukan dadi ya ke idan aka kwatanta da wasu kasashe
- Farashin man fetur ya kara tashi a Najeriya da sauran kasashen duniya ne bayan yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a kasar Iran
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bayelsa - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya da su gode wa Allah cewa farashin mai bai kai tsadar da yake a ƙasar Kenya da sauran ƙasashen Afirka ba.
Hakanna zuwa ne bayan 'yan Najeriya sun cika korafi kan tashin farashin man fetur da ya jawo farashin kayan masarufi suka tashi sosai a fadin kasar.

Kara karanta wannan
DSS ta gano tsohon 'dan majalisa da ya kada hantar Amurka da rashin tsaro a Najeriya

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa Tinubu ya faɗi hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki a lokacin ziyararsa zuwa Jihar Bayelsa, inda ya ƙaddamar da wasu ayyuka.
Ayyukan da Tinubu ya kaddamar a Bayelsa
Daga cikin ayyukan da aka ƙaddamar akwai tashoshin samar da wutar lantarki na gas mai megawatt 60 a Elebele cikin ƙaramar hukumar Ogbia.
Haka zalika akwai gadar Angiama-Oporoma mai tsawon mita 630, titin Sagbama/Ekeremor, da kuma titi mai tsawon kilomita 2.9 a Yenagoa, babban birnin jihar.
Magana kan tsadar man fetur a Najeriya
A cikin jawabin nasa, shugaba Tinubu ya yi martani kan yawan korafin da jama'a ke yi game da tashin farashin man fetur a Najeriya.
Punch ta rahoto ya ce:
“Yana da matuƙar muhimmanci mu kasance masu gaskiya ga mutanenmu. Eh, ina jin korafin ku daga sassa daban-daban na tattalin arziki.
"Farashin mai na matuƙar karuwa, amma ku duba, mu gode wa Allah tare, cewa kun fi samun sauƙi. Ku duba halin da ake ciki a Kenya da sauran ƙasashen Afirka. Ba za mu ja da baya ba. Za mu ci gaba da nemo hanyoyin rage wahalhalun rayuwa.”

Source: Facebook
Me ya kawo tsadar mai a duniya?
Hakan ya biyo bayan toshe mashigar ruwa ta Strait of Hormuz da Iran ta yi, wadda hanya ce da ake bi wajen jigilar mai zuwa sassa daban-daban na duniya.
Sai dai Iran ta amince ta ɗage wannan takunkumi na ɗan lokaci a lokacin tsagaita wuta na mako biyu da ta amince da shi tare da Amurka.
Yaƙin ya fara ne a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, kuma ya ci gaba har zuwa kwanaki kadan da suka gabata lokacin da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta wucin gadi.
An ruguza allunan Tinubu a Ondo
A wani labarin, mun kawo muku cewa wata kungiyar matasa mai goyon bayan APC ta yi korafi kan rusa allunan tallata Bola Tinubu a jihar Ondo.
Shugabannin kungiyar sun bayyana cewa rusa allunan bai dace ba, domin a cewarsu, dimokuradiyya ta ba jama'a 'yancin tallata wanda suke so.
Ta yi kira ga jami'an tsaro a jihar da su dauki mataki kan masu rusa allunan tare da barazanar cewa za su shigar da duk wanda suka kama kotu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
