Sunayen Manyan Jami'an Sojin Najeriya da Suka Mutu a Bakin Aiki daga 2016 zuwa 2026

Sunayen Manyan Jami'an Sojin Najeriya da Suka Mutu a Bakin Aiki daga 2016 zuwa 2026

  • Daga shekarar 2016 zuwa 2026, rundunar sojojin Najeriya ta rasa wasu manya manyan jami'an soji a dai dai lokacin da suke fafatawa da 'yan ta'adda
  • A 2016, rundunar ta girgiza da mutuwar Laftanal Kanal Muhammad Abu Ali, wanda 'yan ta'addar Boko Haram suka kashe a garin Malam Fatori
  • A kwanan nan, an samu labarin kisan Birgediya Janar O. Braimah a Benisheikh; lamarin da ya sa Legit Hausa ta jero manyan sojojin da aka kashe

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Borno - Tarihin yaƙi da ta’addanci a Najeriya, musamman a yankin Arewa maso Gabas, ya nuna yadda manyan jami'an sojojoji suka sadaukar da rayuwarsu a fagen daga.

Ɗaya daga cikin rashin da ya fi girgiza ƙasa shi ne kisan Laftanal Kanal Muhammad Abu Ali a ranar 4 ga Nuwamba, 2016, a garin Malam Fatori.

Kara karanta wannan

Boko Haram: Tinubu ya fadi abin da zai biyo bayan kisan janar a Borno

Fiye da manyan jami'an sojojin Najeriya ne aka kashe a bakin daga daga 2016 zuwa 2026
Sojojin Najeriya sun kame a yayin jana'izar sojojin da aka kashe a harin da aka kai wa ayarin motocin gwamnan Borno, Babagana Zulum a Baga. Hoto: AUDU MARTE/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Kisan Kanal Abu Ali da Kanal Dahiru Bako

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, Abu Ali ya kasance babban jami’i dake jagorantar bataliya ta 272, kuma an yaba masa matuƙa wajen ƙwato garuruwa da dama daga hannun Boko Haram kafin ajali ya cimmasa a wani harin kwanton ɓauna.

Bayan wannan rashi, rundunar sojojin Najeriya ta ci gaba da fuskantar ƙalubale inda wasu manyan jami’ai suka amsa kiran mahalicci a yayin da suke a fagen daga.

A watan Satumban 2020, Kanal Dahiru Chiroma Bako ya rasu sakamakon raunukan da ya ji bayan dakarunsa sun fuskanci harin kwanton ɓauna a kusa da Damboa.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Bako ya shahara wajen jajircewa a yaƙin da ake yi a dajin Sambisa, kuma har shugaban kasa a wancan lokacin ya bayyana shi a matsayin gwarzon soja da ba ya tsoron mutuwa.

Kisan janar-janar din sojojin Najeriya

Kara karanta wannan

Da gaske an kai hari Abuja bayan gargadin Amurka? Gaskiya ta fito

Mafi girman rashi a matakin janar-janar ya faru ne a ranar 13 ga Nuwamba, 2021, lokacin da aka kashe Birgediya Janar Dzarma Zirkusu a garin Askira Uba dake Jihar Borno.

Kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa ta tabbatar, Zirkusu shi ne babban jami’i mafi girman matsayi da aka taɓa kashewa a fagen fama a wancan lokacin.

Ya rasa ransa ne yayin da yake jagorantar dakarunsa don fatattakar mayakan ISWAP da suka kai farmaki garin, wanda hakan ya sa aka karrama shi a matsayin babban jarumin ƙasa.

A cikin shekarun baya-bayan nan na 2025 zuwa 2026, jerin jaruman ya ƙara tsayi da kisan Birgediya Janar M. Uba a ƙarshen shekarar 2025 da kuma na baya-bayan nan, Birgediya Janar O. Braimah, wanda aka kashe a ranar 9 ga Afrilu, 2026, a yankin Benisheikh.

Rahoton jaridar The Cable ya bayyana cewa waɗannan jami’an sun mutu ne yayin gudanar da samamen sintiri da nufin tabbatar da tsaron hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Jerin sunayen manyan jami'an da aka kashe

Rahoto ya nuna cewa an kashe wasu manyan jami'an sojojin Najeriya a lokacin da suke yaki da 'yan ta'adda.
Sojojin Najeriya suna daga hulunan kwanonsu don girmama Shugaba Muhammadu Buhari a ziyarar da ya kai barikin sojoji na Maimalari, Maiduguri a 2021. Hoto: AUDU MARTE/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Ga cikakken jerin manyan sojojin Najeriya da aka kashe a fagen daga, daga shekarar 2016 zuwa 2026, kamar yadda StatiSense ta wallafa a shafinta na X.

Kara karanta wannan

An yi rashi: Yadda 'yan ta'addan ISWAP suka kashe babban Janar da sojoji 17 a Borno

Shekara

Rana

Suna da matsayi

Wurin da kisan ya faru

2016

16 Oktoba

Laftanal Kanal K. Yusuf

Asaga, Jihar Borno

2016

04 Nuwamba

Laftanal Kanal Muhammad Abu-Ali

Malam Fatori, Jihar Borno

2016

15 Nuwamba

Laftanal Kanal B. U. Umar

Hanyar Bitta-Pirang, Adamawa

2016

12 Disamba

Laftanal Kanal O. Umusu

Gudumbali, Jihar Borno

2018

18 Nuwamba

Laftanal Kanal Ibrahim Sakaba

Arewacin Jihar Borno

2020

21 Satumba

Kanal Dahiru Chiroma Bako

Damboa (Wajirko), Borno

2020

24 Satumba

Laftanal Kanal M. Z. Manu

Jihar Katsina

2021

13 Nuwamba

Birgediya Janar Dzarma Zirkusu

Askira Uba, Jihar Borno

2025

17 Nuwamba

Birgediya Janar M. Uba

Kusa da Wajiroko, Borno

2026

09 Afrilu

Birgediya Janar O. Braimah

Benisheikh, Jihar Borno

Martanin Tinubu kan kisan Janar Braimah

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin murkushe ta’addanci bayan harin da ya kashe Birgediya Janar O. Braimah a jihar Borno.

Shugaban ya bayyana haka ne bayan sojoji sun dakile farmakin ‘yan Boko Haram a Benisheikh, amma an yi asarar rayuka da dama.

Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa rashin babban jami'in sojin ba zai sare ayyukan rundunar sojin kasar nan ba wajen yakar yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com