Abubuwan mamaki game da jarumtar Abu Ali

Abubuwan mamaki game da jarumtar Abu Ali

- A wani yanayi da ba’a taba gani ba, Babban Hafsan sojin Najeriya Janar Tukur Buratai ya zub da hawaye a yayin binne 

- Kanar Muhammadu Abu Ali, watakila hakan ba zai rasa nasaba da fadin Hausawa ba da ke cewa, ba  rabo da gwani ba, sai dai da wuya a mayar da kamarsa, ga kadan daga cikin jarumtakar marigayin da ya sa har yanzu Najeria ke alhinin rashinsa

Abubuwan mamaki game da jarumtar Abu Ali
Lt col Abu Ali

1. Sarkin Yaki

A dalilin Jarumtar marigayin ne ‘yan uwansa sojoji suka yi masa lakabi da ‘sarkin yaki’ a fagen daga, a ta’aziyyar daya daga cikin sojojin da Kanar Abu Ali ya jagoranta yana mai cewa, “kanar Ali ne ya jagoranci kwato yawancin garuruwan da suke hannun ‘yan Boko Haram tun daga bangaren Yola, cikin har da Konduga, da Damboa, sannan ya shi ya jagoranci kwato Monguno da kuma Baga”.

2. Kwazo da rashin tsoro

A bayanin kwazo da rashin tsoron marigayin, Soja na cewa, “Yayin da ‘yan ta’adda suka sa mu a gaba, mun kuma kasa gaba, mun kasa yin baya, sai aka turo mana kai daga Konduga, da zuwanka sai labari ya sha baban-ban, a inda da ka shiga gaba, da yardar Allah sai da muka kwato Yale, da Bama, da Banki, da Pulka, da kuma Gwoza.

KU KARANTA KUMA: Buratai ya zub da hawaye a jana’izar Abu Ali

Sojan ya ci gaba cewa, “Na tuna lokacin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka harbawa tankin yakinka mai sulke curin albarushi samfurin 'Howitzer pack'  mai girman 105mm, a lokacin da suka yi amfani da VIED don tarwatsa motar yakinka, a lokacin yakin kwato Gwoza, mun dauka ka mutu, ashe da sauran kwana, amma da jin muryar ka a na’urar oba-oba, ba mu lokacin da muka barke da ihu da sowa ba, kuma hakan da ka yi, ya kara mana karfin gwiwa da ci gaba da fafatawa.

 3. Sadaukar da kai

“Ba zan taba mantawa da kalaman da ka ke fada mana ba a filin daga, ka na cewa, ‘Ku biyo ni a baya, ku yi aikin kashi 5 kacal, ni zan yi ragowar 95’"

4. Gwarzon Sambisa

“Kai ne soja na farko da ka keta dajin Sambisa bayan ka jagoranci kawato Yemteke, garin Bita kuwa ta gagari kowa. Kai ne na farko da ka kutsa dajin ka kuma ceto mata 296 daga hannun Boko Haram. Jirgin sama mai saukara ungulu aka aika, ya daukoka daga nan, domin ka shige gaba wajen kwato Gamborun Ngala. Aikin da kayi ba gajiyawa."  

5. Lambar Yabo

Kanar Ali shine kwamandan tankuna yaki na sojin ta wata Bataliya da ke yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, ya kuma samu lambar yabo ta nuna jarumta a fagen yaki ta Babban Hafsan sojojin Najeriya a shekarar 2015.

6. Karin girma kan girma

An karawa Muhammad Abu Ali girma kan girma zuwa Manjo da laftanar Kanar, saboda kwazo da jarumta.

Allah Ya jikan maza

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng