APC na tsakiyar Zawarcin Shekarau, Tinubu Zai Narka kusan Naira Biliyan 4 a Kano
- Gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta amince da kashe N3.8bn domin gina tashar wutar lantarki ta sola mai ƙarfin 2MW a jami'ar Aliko Dangote, Kano
- Aikin na cikin shirin "Renewed Hope" wanda ke mayar da hankali kan samar da wuta a manyan makarantu da asibitoci a fadin ƙasar nan
- Jami'ar ADUST ta roki gwamnati da ta samar da dakin gwaje-gwajen makamashi da kuma horar da ɗalibai kan fasahohin zamani na makamashi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano – Gwamnatin Bola Tinubu ta bayar da kwangilar gina tashar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai ƙarfin megawatt biyu a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, Jihar Kano.
Wannan gagarumin aiki da gwamnatin za ta gudanar, zai lashe kimanin Naira biliyan 3.8, kamar yadda sanarwa ta fito daga hannun Mataimakin magatakardan jami'ar, Abdullahi Abdullahi.

Source: Twitter
Gwamnatin Tinubu za ta yi aikin N3.8bn a Kano
Sanarwar ta ce shugaban hukumar makamashi ta Najeriya (ECN), Dr. Mustapha Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi bakuncin shugaban jami'ar, Farfesa Musa Yakasai, a ranar Laraba a Abuja, in ji rahoton Punch.
A cewar Dr. Mustapha Abdullahi, Ma'aikatar kimiyya da fasaha ta riga ta bayar da kwangilar, kuma za a fara aikin nan ba da jimawa ba.
Shugaban hukumar makamashin ya jaddada cewa wannan aiki na cikin shirin "Renewed Hope" na Shugaba Bola Tinubu, wanda zai samar da wutar lantarki ta sola zuwa asibitoci, manyan makarantu, da yankunan karkara a faɗin ƙasar.
"Kwangilar gudanar da wannan aiki, wadda tuni ma'aikatar kirkira, kimiyya da fasaha ta tarayya ta bayar da ita, za ta lakume N3.8bn, kuma za a fara aiwatar wa nan ba da jima wa ba."
- Dr. Mustapha Abdullahi.
Za a kafa fitilu 200 a jami'ar ADUST
Ya bayar da misali da yadda shugaban ƙasar ya amince da gina tashar sola ta 4MW a asibitin AKTH da ke Kano bayan fuskantar ƙalubalen rashin wuta.
Haka kuma, shugaban hukumar ya sanar da cewa za a sake aika fitilun titi guda 200 zuwa jami'ar domin ƙarawa a kan guda 200 da aka bayar a baya.
Wannan mataki zai inganta tsaro da samar da yanayi mai kyau ga ɗalibai, domin su yi karatu cikin kwanciyar hankali har a lokacin dare.

Source: Twitter
Martanin jami'ar Aliko Dangote
A nasa ɓangaren, Shugaban jami'ar ADUST, Farfesa Musa Yakasai, ya jinjina wa shugaban hukumar bisa irin gudunmawar da yake ba wa makarantar, in ji rahoton Solace Base.
Ya bayyana cewa fitulun titin da aka bayar a baya sun taimaka ƙwarai wajen inganta tsaron harabar jami'ar da kuma sauƙaƙa wa ɗalibai karatu.
Yakasai ya taya Dr. Mustapha murnar naɗin sa da shugaban ƙasa ya yi, sannan ya yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jami'ar da hukumar ECN.
Ya buƙaci a ba da fifiko wajen samar da dakin gwaje-gwajen makamashi da kuma horar da ɗalibai kan fasahohin zamani na makamashi.
Wannan dai na zuwa ne yayin da jam'iyyar APC ke ci gaba da zawarcin tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, da nufin kara karfinta gabanin zaben 2027.
Za a gina tashar sola a Aso Rock
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnati ta bayyana cewa tana shirin girka tashar sola a Aso Villa don rage yawan kuɗin wutar lantarki da take biya.
Shugaban hukumar makamashi ta kasa ya ce gwamnati na kashe Naira biliyan 47 duk shekara a kudin wutar fadar Aso Rock.
Domin rage kashe kudin gwamnati, an ce Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 10 don gina karamar tashar sola a cikin fadar.
Asali: Legit.ng


