Bayan an Kama Su da Ta'addanci, Kotu Ta Sanar da Ƴan Boko Haram 18 Makomarsu

Bayan an Kama Su da Ta'addanci, Kotu Ta Sanar da Ƴan Boko Haram 18 Makomarsu

  • Kotun tarayya da ke babban birnin Abuja ta yanke wa mambobin Boko Haram 18 hukunci bayan sun amsa laifi
  • Kotun ta yanke wa mutum hudu hukuncin daurin rai da rai, yayin da sauran aka yanke musu shekaru 20 zuwa 25
  • Gwamnatin tarayya ta ce ana gurfanar da mutane 500 da ake zargin sun aikata ta'addancina matakai daban-daban

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutum hudu da ake zargi ƴan kungiyar Boko Haram hukuncin daurin rai da rai bayan sun amsa laifuffukan da ake tuhumar su da su.

Alkalin kotun, James Omotosho, ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, 7 ga watan Afrilu, 2026 inda ya kuma yanke wa wasu mutum 14 hukuncin zaman gidan yari tsakanin shekaru 20 zuwa 25 bisa laifufukka daban-daban.

Kara karanta wannan

Bayan Iran, gwamnatin Trump ta juyo Najeriya, ta yi gargadi kan tsaro

An hukunta ƴan Boko Haram a Abuja
Wasu daga cikin sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

The Cable ta wallafa cewa shari’ar ta biyo bayan yadda wadanda ake tuhuma suka amsa laifuffukansu a gaban kotu, yayin da wani shaida daga DSS ya gabatar da hujjoji da suka goyi bayan karar gwamnati.

Kotu ta hukunta ƴan Boko Haram

Channels TV ta wallafa cewa babban lauyan gwamnati, wato Antoni Janar na Tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi, tare da daraktan shari’ar gwamnati Rotimi Oyedepo, sun gabatar da rahotannin bincike a matsayin hujjoji.

Mutanen da aka yankewa daurin rai da rai sun hada da Ali Abiso, Bakura Abah Kabiru, Ado wanda aka fi sani da Luka Garba, da kuma Babagoni Masawai.

A cikin karar da aka shigar mai lamba FHC/KNJ/CR/509/2026, Ali Abiso shi kadai ne wanda ake tuhuma, kuma ya amsa dukkannin tuhume-tuhume guda hudu da ake masa.

Kara karanta wannan

"Idonmu na kan ku": Kwankwaso ya tura sako bayan zanga zangar adawa da matakin INEC

Gwamnati ta bayyana cewa Abiso mai shekaru 30 daga karamar hukumar Bama a jihar Borno ya shiga cikin hare-haren da aka kai a Bama, Gwoza, Konduga, Bita, Baza da Aulari kafin ranar 8 ga Yulin 2022.

Alkalin ya yanke masa daurin rai da rai a wasu tuhume-tuhume biyu, sannan ya kara masa shekaru 25 a wasu tuhume-tuhume biyu, inda ya umarci a yi hukuncin tare.

Sauran ƴan Boko Haram da aka daure

Kotun ta kuma yanke wa Kabiru daurin rai da rai a wani laifi tare da karin shekaru 25 saboda wasu laifuffuka biyu. Haka zalika Ado ya samu daurin rai da rai a laifi guda, tare da shekaru 25 a wani.

Shi kuma Masawai, an yanke masa daurin rai da rai a tuhume-tuhume biyu, sannan aka kara masa shekaru 20 a wasu laifuffukan biyu, da kuma shekaru 10 a wasu uku.

Gwamnati ta ce ana ci gaba da shafia da wasu ƴan ta'adda
Mashawarcin shugaban ƙasa a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Facebook

Sauran mutum 14 da suka amsa laifi sun samu hukunci daban-daban bisa girman laifuffukansu, inda aka yanke masu hukunci bayan an gamau da hujjojin da aka gabatar a kotun.

Daga cikinsu akwai Ali Mustapha wanda aka yanke masa shekaru 20 a laifi guda, da kuma shekaru 10 a wasu laifuffuka shida, jimillar shekaru 80, amma kotu ta umarci a yi hukuncin tare.

Kara karanta wannan

Yakin Iran/Isra'ila: Yawan asarar da Amurka ta yi yayin yaki a Gabas ta Tsakiya

Sauran wadanda aka yankewa hukunci sun hada da Danbawa Salisu, Modu Ali, Sanda Bello, Mustapha Fali, Modu Musa, da Bidal Modu.

Sai kuma Mohammed Abdullahi, Umar Garba, Usman Ahmadu, Hussaini Bukar, Baba Manye, Musa Mai Modu da Ali Musa.

Ministan shari’a ya bayyana cewa ana ci gaba da gurfanar da mutane 500 a mataki na tara na shari’ar manyan masu laifi da ake zargi da ta’addanci a Abuja.

An kama ɗan Boko Haram

A baya, kun ji cewa dakarun Najeriya sun kama wasu mutane da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne da ke kai hare-hare a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Daga cikin wadanda aka kama akwai mai suna John Ado da ya amsa cewa yana tallafawa kungiyar, inda ya fadi wuraren da suka kai hari a yankin.

John Ado ya bukaci jami'an tsaro su sake shi domin a cewar shi ya tuba, kuma zai ba gwamnati hadin kai wajen tona asirin 'yan ta'addan da suka rika aiki tare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng