Bayan Iran, Gwamnatin Trump Ta Juyo Najeriya, Ta Yi Gargadi kan Tsaro
- Kasar Amurka ta sake fitar da rahoto game da yanayin tsaro a Najeriya bayan yawaitar garkuwa da mutane da kai hare-hare kan al'umma
- Sanarwar da ta fitar ta nuna cewa kasar za ta kwashe wasu jami'anta tare da iyalansu da ke aiki a ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja
- Ta kuma bayyana wasu jihohi da suka hada da Filato, Taraba da Yobe, inda ta ce babu zaman lafiya tare da gargadin 'yan kasarta kan zuwansu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ba da izini ga ma’aikatan gwamnati da ba su aikin gaggawa da iyalansu su bar ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja, tana mai nuni da tabarbarewar tsaro a fadin Najeriya.
A cikin sabon gargadin tafiye-tafiye da aka fitar a ranar Laraba, ma’aikatar ta bayyana cewa daga ranar 8 ga Afrilu, 2026, ana shawartar ‘yan Amurka su sake tunanin tafiya zuwa Najeriya.

Kara karanta wannan
Tun ba a je ko'ina ba, Shugaba Trump ya canza tsarin tattaunawar Amurka da kasar Iran

Source: Getty Images
A sakon da ta wallafa a shafin yanar gizo, Amurka ta ce ta yi gargadin ne saboda matsalolin, ta’addanci da nau'ukan tashin hankali da ake fama da su a kasar nan.
Jihohin da Amurka ta yi gargadi a kansu
Amurka ta ambaci jihohin Plateau, Jigawa, Kwara, Niger da Taraba cikin jerin wuraren da take gargadi game da zuwansu, wanda ya kawo adadin jihohin zuwa 23 da ake gargadin kauce musu.
Jihohin da aka shawarci ‘yan Amurka su guje wa zuwa a Arewa sun hada da Borno, Jigawa, Kogi, Kwara, Niger, Plateau, Taraba, Yobe da kuma Arewacin Adamawa, saboda ta’addanci da garkuwa da mutane.
Punch ta wallafa cewa sanarwar ta kuma lissafo Bauchi, Gombe, Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto da Zamfara, tana nuni da samun tashin hankali da garkuwa da mutane.

Source: Original
“Yanayin tsaro a wadannan jihohi ba shi da tabbas kuma yana canzawa sakamakon tashin hankalin da ake fama da shi. Akwai rikice-rikicen al’umma da masu aikata laifuffuka da ke dauke da makamai, ciki har da garkuwa da mutane da fashi."
Inji sanarwar.
Gargadin Amurka kan jihohin Kudu
A kudancin Najeriya, ma’aikatar ta bukaci ‘yan Amurka su guji jihohin Abia, Anambra, Bayelsa, Delta, Enugu, Imo da Rivers (ban da Port Harcourt), saboda garkuwa da mutane da tashin hankali.
“Laifuffuka sun yadu a Kudancin Najeriya. Akwai babban hadarin garkuwa da mutane, zanga-zanga mai tashin hankali da kuma kungiyoyin ‘yan daba masu dauke da makamai,”
In ji sanarwar da Amurka ta fitar.
Amurka ta yi gargadi kan zuwa Hajji
A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin Amurka ta fitar da gargadi game da zuwa aikin Hajjin shekarar 2026 ga 'yan kasarta.
Hakan na zuwa ne bayan hare-haren da aka kai kasashen Gabas ta Tsakiya da suka hada da kasar Saudiyya da ake yin aikin a cikinta.
Duk da cewa an tsagaita wuta a yakin, babu tabbas ko zaman da za a yi a Pakistan tsakanin Amurka da Iran zai kai ga samun nasara.
Asali: Legit.ng
