Jerin Jihohin Najeriya 14 Da Amurka Ta Ce Matafiya Su Kaurace Musu, Hukumomin Leken Asiri Sunyi Martani

Jerin Jihohin Najeriya 14 Da Amurka Ta Ce Matafiya Su Kaurace Musu, Hukumomin Leken Asiri Sunyi Martani

  • Kuma, Amurka ta sake fitar da wani shawarwari na gargadi game da rashin tsaro a wasu jihohin Najeriya
  • Amurka ta gargadi matafiya game da zuwa wasu jihohin Najeriya 14 daga arewa maso gabas, arewa maso yamma da kudu maso kudu
  • Amma, hukumomin leken asiri na Najeriya sun ce wannan ikirarin cewa wani mataki ne na kawo cikas ga kokarin hukumomin tsaron Najeriya

FCT Abuja - Kwana uku bayan fitar da gargadin kai harin ta'addanci, wani sabon rahoto ya ce Amurka ta bada shawarwari ga yan Najeriya don kare kansu.

Kamar yadda PRNigeria ta rahoto, a cikin shawarar ta baya-bayan nan, Amurka ta gargadi matafiya game da ziyartar jihohi 14 cikin 36 na Najeriya.

Jami'an DSS
Jerin Jihohin Najeriya 14 Da Amurka Ta Ce Matafiya Su Kaurace Musu, Hukumomin Leken Asiri Sunyi Martani. Hoto: DSS
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari

Sun ce garkuwa da mutane, ta'addanci, yan fashin teku da tada hankali na fararen hula sunyi yawa a jihohin.

Hukumomin leken asirin Najeriya sunyi martani

A martaninsu, wani jami'in hukumar leken asiri na Najeriya wanda ya yi magana da jaridar ya ce wannan rahoton da Amurka da Birtaniya ke yadawa wani yunkuri ne na dakile kokarin hukumomin leken asirin da na tsaro.

Majiyar ta ce:

"Tuni, hukumomin tsaro sun yi abin azo-a-gani a kwana-kwanan nan, a bangaren kama kwamandojin yan ta'adda, halaka mayakansu, da sauraron maganganun da suke yi a waya.
"Abin takaici ne a yayin da muke raba shawarwarin tsaro da ofisoshin jakadanci kan tsaro, kamar yadda a wasu lokuta muke sanar da jama’a, wadanna kasashen waje suna amfani da hakan wajen kawo cikas ga kokarinmu na kawo tsaro."

Jerin jihohin da Amurka ta bada shawarar matafiya su kaurace musu

Kamar yadda aka gani a rahoton PRNigeria, jihohi 14 da Amurka ta bada shawarar matafiya su kaurace musu sune:

Kara karanta wannan

Bayan Amurka, Manyan Kasashen Duniya 3 Sun gano Yiwuwar kai hari a Birnin Abuja

Arewa Maso Gabas

1. Borno

2. Yobe

3. Adamawa

4. Bauchi

5. Gombe

Arewa Maso Yamma

6. Kaduna

7. Kano

8. Katsina

9. Zamfara

Kudu Maso Kudu

10. Akwa Ibom

11. Bayelsa

12. Cross River

13. Delta

14. Rivers

Bayan Amurka, Manyan Kasashen Duniya 3 Sun gano Yiwuwar kai hari a Birnin Abuja

A bangare guda, Hukumomin Australiya da Kanada sun gargadi mutanensu a game da yin tafiya zuwa Najeriya a daidai wannan lokaci.

Daily Trust ta ce wannan gargadi yana zuwa ne kusan kwanaki uku bayan Amurka da Ingila sun gano barazanar rashin tsaro a kasar.

A tsakiyar makon nan aka ji Gwamnatin Australiya ta ba ‘yan kasar ta shawara da su hakura da zuwa kasar Najeriya a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel