2027: Matasa Sun Yi wa Gidan Tsohon Shugaban Ƙasa Tsinke, Ana So Ya Nemi Kujerar Tinubu
- Daruruwan matasa sun yi wa gidan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a Abuja dafifi a kan batun 2027
- Masu zanga-zangar sun ce sun yi shawarwari a fadin ƙasa kafin neman Jonathan ya dawo kujerarsa
- Jonathan bai gana da matasan ba, amma ana ci gaba da matsa masa lamba ya dawo siyasa a dama da shi a zaɓen 2027
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Daruruwan matasa ƙarƙashin ƙungiyar Coalition for Goodluck Jonathan sun yi gangami a ranar Laraba, 9 ga watan Afrilu 2050, inda suka ziyarci gidan sohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, da ke Abuja.
Matasan sun buƙaci Jonathan da ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 da ke karatowa a ƙasa da watanni 12 masu zuwa.

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta wallafa cewa gangamin ya gudana ne a Titin Taraba Close da ke unguwar Maitama a Babban Birnin Tarayya, inda ya jawo cunkoson ababen hawa.
Matasa sun ziyarci gidan Goodluck Jonathan
The Guardian Nigeria ta wallafa cewa a yayin da matasan suka ziyarcigidan Jonathan, sun rika rera waƙoƙi, suka sha rawa da kuma daga allunan da ke ɗauke da saƙonnin kira ga Jonathan ya dawo siyasa.
Wasu daga cikin saƙonnin sun haɗa da:
“GEJ: Najeriya na cikin hali mai wuya, ka ceci ƙasa!”
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Tom Ohikere, wanda ya jagoranci gangamin, ya bayyana cewa sun shafe watanni shida suna tuntubar jama’a a sassa daban-daban na ƙasar kafin su shirya wannan tattaki.

Source: Twitter
Ya ce:
“A duk inda muka je yayin wannan tuntuba ta ƙasa na tsawon watanni shida, mun ji kira mai ƙarfi da babu shakka na mutane suna son ya dawo mulki domin ceto ƙasar nan.”
Ana son Jonathan ya dawo siyasa
Ohikere ya ƙara da cewa suna kallon Jonathan a matsayin jagora mai haɗa kan al’umma wanda zai iya tunkarar matsalolin siyasa da tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta a yanzu.
Ya kuma jaddada cewa za su ci gaba da matsa masa lamba har sai ya amsa, ya bayyana aniyar zai tsaya takarar zaben 2027.
Duk da cewa matasan sun jira fiye da sa’o’i uku a wajen gidan, ba su samu damar ganawa da Jonathan ba, domin an ce ba ya gida ba a lokacin.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa ya isa gidan da misalin ƙarfe 1 na rana, bayan da masu zanga-zangar suka riga suka watse.
Wannan gangami na zuwa ne yayin da ake ƙara samun kiraye-kiraye daga ƙungiyoyin siyasa da ma ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje da ke roƙon Jonathan ya dawo harkokin siyasa kafin zaɓen 2027.
Atiku ya ziyarci Jonathan
A baya, mun wallafa cewa an yi ta rade-radi da 'yan kunji-kunji bayan Atiku Abubakar ya yi zama da tsohon shugaban kasar Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ziyarci Goodluck Jonathan ne a gidansa da ke Abuja kwanaki bayan ya dawo daga kasar Guinea-Bissau.
Hadimin tsohon shugaban kasar Paul Ibe, ya bayyana dalilin da ya sa Atiku ya ziyarci Jonathan bayan an fara yada cewa ziyarar na da alaka da siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


