2027: Majalisar Shari'ar Musulunci da Kungiyoyi 3 da Suka Nemi a Canza Shugaban INEC
Abuja, Nigeria - A watan Oktoba, 2025 ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jaosh Amupitan, wanda ya kasance kwararren lauya da ya kai matsayin SAN a Najeriya, ya maye gurbin tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, wanda wa'adinsa na biyu ya kare.

Source: Facebook
Yadda Joash Amupitan ya karbi shugabancin INEC
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin Facebook, ya ce Amupitan ya karbi rantsuwar kama aiki ne a ranar 23 ga Oktoba, 2026.
Shugaba Tinubu ne ya jagoranci rantsar da Farfesa Amupitan a matsayin sabon shugaban INEC bayan ya tsallake duk wani matakin tantancewa da doka ta tanada.
An taso sabon shugaban INEC a gaba
Sai dai tun bayan kama aikinsa, Farfesa Amupitan ya fara fuskantar matsin lamba daga sassa daban-daban na kasar nan musamman 'yan adawa da kuma kungiyoyin addini.
Amupitan ya tsinci kansa a wani yanayi bayan bullar wata takardar da ake zargin ya rubuta kuma ya aika zuwa kasar Amurka da Majalisar dinkin duniya da nufin kai korafin kisan kiristoci.
Wasu daga cikin kungiyoyin addinin musulunci a Najeriya sun nuna damuwa kan abubuwan da ya rubuta a takardar, inda suke ganin ga dukkan alamu ba zai wa musulmi adalci ba, don haka suka nemi ya yi murabus.
Manyan kungiyoyin da suka nemi canza Amupitan
A wannan rahoton, mun tattaro muku kungiyoyi, da yan siyasar da suka nemi Shugaban INEC, Farfesa Amupitan ya yi murabus tare da hujjojin da suka gabatar.
1. Majalisar shari'a ta Najeriya
Majalisar ƙoli kan harkokin shari'ar musulunci a Najeriya (SCSN) karkashin jagorancin Dr. Bashir Umar Aliyu ta yi kira ga shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ya yi murabus.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito kan zargin Tinubu da haddasa rikicin ADC bayan hadewar Atiku, Obi da Kwankwaso
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar, wadda sakatarenta na kasa, Nafi’u Baba Ahmad ya sanya wa hannu, kamar yadda BBC Hausa ta kawo.
Majalisar ta kuma karyata rade-radin cewa bukatar da ta mika ta a gaggauta cire shugaban INEC tana da alaka da addini, inda ta ce hakan ba gaskiya ba ne.

Source: Facebook
Ta ce dalilin neman cire Farfesa Amupitan yana da alaƙa da wasu abubuwa da ya aikata a baya, musamman wata takarda da ya jagoranci rubutawa a 2020.
A cewarta, a cikin takardar ya yi amfani da kalamai masu zafi da cin mutunci ga musulman Najeriya, yankin Arewa da Shehu Usman Ɗanfodio.
Ta ce a cikin takardar, ya yi zargin ana yi wa Kiristocin Najeriya “kisan kiyashi”, sannan ya yi yunƙurin alaƙanta matsalar tsaro da jihadin Ɗanfodio na ƙarni na 19, abin da majalisar ta ce yunƙuri ne na tayar da zaune tsaye.
2. Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC)
A nata bangaren, Kungiyar Kare Haƙƙin Musulmi ta Najeriya (MURIC) ta fito ta bayyana cewa bai kamata Farfesa Amupitan ya ci gaba da zama a kujerar shugaban INEC ba.
MURIC ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsige Farfesa Amupitan daga mukaminsa saboda ra’ayinsa kan batun tsaron kasar nan.
Kungiyar ta dauko wasu bangarori na takardar da Amupitan ya rubuta, musamman inda ya ce ana kokarin musuluntar da Najeriya ta hanyar kokarin karar da kiristoci.

Source: Twitter
Daily Trust ta ce a wata sanarwa da Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar, kungiyar ta bayyana cewa:
“Mutumin da ya rubuta wasiƙa mai cike ƙiyayya ga Shugaba Donald Trump yana zargin Musulmai a Arewacin Najeriya, ba za a iya aminta da shi wajen jagorantar zaɓe ba."
3. Tafiyar hadaka, ADC
Tafiyar hadaka a karkashin jam'iyyar ADC ta yi kira da a sauke Farfesa Joash Amupitan daga kujerar shugaban hukumar INEC na kasa saboda zarginsa da yunkurin maida Najeriya tsarin jam'iyya daya.
Shugaban ADC na kasa, Sanata David Mark ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka shirya a Yar’Adua Centre da ke Abuja a makon jiya, kamar yadda This Day ta rahoto.

Source: Facebook
Wannan kira na zuwa ne bayan INEC ta goge sunayen shugabannin ADC na tsagin David Mark saboda shari'ar da ke gaban kotu.
4. Kungiyar Izala ta Jos
Shugaban Majalisar Malamai na Ƙungiyar Jama’atuI Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) mai hedkwata a Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya nemi a sauya shugaban INEC.
A wani rahoto da Daily Post ta wallafa, Malamin Musuluncin ya bayyana naɗin Farfesa Joash Ojo Amupitan a matsayin babban hadari ga Najeriya.
A cewarsa, Musulman Najeriya ba su aminta da naɗin Amupitan ba, ganin irin rubuce-rubucen da ake dangantawa da shi a baya na kokarin kakaba zargin kisan Kiristoci a Najeriya.

Source: Facebook
INEC ta hango matsala a zaben 2027
Kun ji cewa Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ya yi gargaɗin cewa yaɗa bayanan ƙarya na iya zama babban haɗari ga babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027.
Amupitan ya ce a halin yanzu ana yanke makomar sakamakon zaɓe ne a "wuraren yaɗa labarai," wanda hakan ya sa rawar da gidajen rediyo da talabijin ke takawa ta kasance mai matuƙar muhimmanci.
Shugaban INEC ya bayyana cewa akwai rawar da kafafen yada labarai za su taka wajen ciyar da dimokuradiyyar Najeriya gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


