Halin da Mazauna Iran Ke Ciki bayan Sanar da Tsagaita Wuta tsakanin Kasar da Amurka

Halin da Mazauna Iran Ke Ciki bayan Sanar da Tsagaita Wuta tsakanin Kasar da Amurka

  • Mazauna Tehran sun fito kan tituna suna murna bayan sanar da tsagaita wuta na makonni biyu tsakanin Amurka da Iran
  • Jama’a sun daga tutocin kasa suna rera taken adawa da Amurka da Isra’ila, yayin da wasu ke yabon rawar da Pakistan ta taka wajen sasanta yarjejeniyar
  • Ministan harkokin wajen Iran ya ce sojoji za su dakatar da hare-hare idan aka daina kai farmaki, da damar zirga-zirga cikin kwanciyar hankali a mashigin Hormuz

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Bayan fiye da wata ana rikici mai tsanani, mazauna Tehran sun yi murna bayan sanar da tsagaita wuta.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na makonni biyu tsakanin Amurka da Iran bayan shafe fiye da wata ana yaki.

Ana murna a Iran kan shirin tsagaita wuta
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump. Hoto: Imam Sayyid Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

Bidiyoyi da Al Jazeera ta samu sun tabbatar cewa jama’a suna daga tutocin Iran suna murna a babban birnin Tehran.

Kara karanta wannan

Shirin tsagaita wuta tsakanin Iran, Amurka ya kawo gagarumin sauyi a duniya

Yadda yakin Iran, Isra'ila ya barke

Wannan na zuwa ne bayan barkewar yaki tsakanin Iran da kasar Isra'ila da ke samun goyon bayan Shugaba Donald Trump na Amurka.

An fara yakin ne a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 wanda ya yi sanadiyar mutuwar jagoran addini a kasar, Ayatollah Ali Khamenei.

Iraniyawa sun barke da murna a Tehran

Har ila yau, mutane sun taru a manyan tituna duk da cewa ba a tabbatar da wasu hotunan da ake yada wa game da taron ba.

Jama’a sun taru a sassa daban-daban na birnin suna rera wakoki da daga tutoci, suna bayyana hakan a matsayin nasara, yayin da ake yabon rawar Pakistan wajen sulhu.

Rahotanni sun nuna wasu masu zanga-zanga na rera taken adawa da Amurka da Isra’ila, alamar cewa har yanzu akwai matsalolin siyasa duk da tsagaita wutar da aka cimma.

Martanin Iran kan tsagaita wuta da Amurka

Ministan harkokin wajen Iran, Seyed Abbas Araghchi, ya ce sojojin kasar za su dakatar da ayyukan kare kai idan aka daina kai musu hari gaba daya, kamar yadda TRT Africa ta wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Iran ta fitar da sanarwa da Amurka ta yarda ta tsagaita wuta da kasar Musulunci

Ya kuma kara da cewa Iran za ta ba da damar wucewa lafiya ta mashigin Hormuz na tsawon makonni biyu, tare da hadin gwiwar rundunonin tsaro na kasar.

Duk da cewa tsagaita wutar na wucin gadi ne, yana ba da damar samun sauki daga rikici da kuma bude kofar tattaunawa domin samun zaman lafiya mai dorewa.

Har yanzu babu cikakken bayani kan matakan da za a dauka bayan wannan wa’adi, lamarin da ke barin tambaya kan ko za a iya cimma yarjejeniya ta dindindin.

Isra'ila ta magantu bayan kai mata hari

A wani labarin, an ji cewa rahotanni da dama sun bayyana an kashe mutum daya yayin harin bindiga kusa da ofishin jakadancin kasar Isra’ila.

‘Yan sanda biyu sun jikkata yayin da jami’an tsaro suka shiga yankin bayan harbin bindiga yayin da ake yaki a Gabas ta Tsakiya.

Isra’ila ta yi gargadin karuwar barazanar hare-hare kan ‘yan kasarta a kasashen waje inda ta bayyana shirin daukar matakai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.