NiMet: Za a Sheka Ruwan Sama a Kaduna, Taraba da Wasu Jihohi a Ranar Laraba

NiMet: Za a Sheka Ruwan Sama a Kaduna, Taraba da Wasu Jihohi a Ranar Laraba

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama da tsawa a wasu jihohin Arewa da Kudu a safiya da yammacin ranar Laraba
  • Kudancin Najeriya ne zai samu ruwan sama mai yawa, inda ruwan zai sauka a kusan dukkan jihohin shiyyar, a cewar rahoton NiMet
  • NiMet ta gargadi masu fama da cututtukan numfashi da su takaita zirga-zirga waje, sannan direbobi su yi taka tsantsan da yayin da ake ruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta Najeriya, watau NiMet, ta fitar da hasashen yanayin da za a tashi da shi a gobe Laraba, 8 ga Afrilu, 2026.

NiMet ta yi hasashen cewa za a samu yanayin kura da hazo a wasu sassan ƙasar, yayin da wasu sassan za su fuskanci ruwan sama da iska.

Kara karanta wannan

An kwantar da Trump a asibiti bayan kamuwa da rashin lafiya? An samu gaskiya

NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama a wasu jihohin Najeriya ranar Laraba
Ruwan sama da iska mai karfi na sauka a wani sashen Najeriya. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

Hasashen yanayi a wasu jihohin Arewa

Wannan na kunshe ne a cikin rahoton hasashen yanayi da NiMet ta fitar a shafinta na X a yammacin ranar Talata, 7 ga watan Afrilu, 2026.

A safiyar Laraba, ana sa ran cewa za a samu samu matsakaiciyar iska mai dauke da kura wadda za ta iya rage hangen nesa ga matafiya a jihohin Borno, Yobe, Kano, Katsina, Zamfara, Jigawa, Kebbi, da Sokoto.

Da yamma kuwa, za a iya samun ruwan sama hade da tsawa a wasu sassan jihohin Taraba, Bauchi, Kaduna, Adamawa, da Gombe yau.

Idan aka leka Arewa ta tsakiya kuwa, NiMet ta yi hasashen cewa za a samu hadari, amma rana za ta fito tangaran, a jihohin Neja, Kwara, da Kogi.

Idan yamma ta yi kuma, ana hasashen samun ruwan sama zai sauka a jihohin Nasarawa, Plateau, Kwara, Kogi, Benue, har ma da babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Kasashen Afirka 3 da kasar Isra’ila ta taɓa kai masu farmaki a baya

Hasashen yanayin ruwa a jihohin Kudu

Hasashen NiMet ya nuna cewa za a samu haduwar hadari da kuma saukar ruwan sama da tare da tsawa a jihohin Oyo, Osun, Ekiti, Ogun, Ondo, Edo, Legas, Cross River, Akwa Ibom, Bayelsa, Rivers, da Delta.

Da yammacin ranar ta Laraba, ruwan sama da tsawa za su karu a daukacin yankin Kudu, wanda hakan zai janyo santsin titi da kuma rage gani ga matafiya, a cewar NiMet.

NiMet ta ba 'yan Najeriya shawarwari yayin da ake sa ran ruwan sama zai sauka a ranar Laraba.
Shugaban hukumar NiMet da wasu ma'aikata na kafa na'urorin hasashen yanayi a Abuja. Hoto: @nimetnigeria
Source: Twitter

Shawarwarin NiMet ga 'yan Najeriya

Hukumar NiMet ta ba da waɗannan shawarwari domin kiyaye kai yau:

  • Kura na iya shafar masu ciwon 'asama' ko sauran matsalolin numfashi, don haka mutane su rage fita waje.
  • Iska mai ƙarfi na iya kaɗawa kafin ruwa ya fara, don haka a tabbatar an killace abubuwan da iska kan iya ɗauka.
  • Direbobi su rage gudu saboda rashin gani da kuma santsin titi, don guje wa afkuwar hadurra.
  • A guji shiga wuraren da ruwa ke yawan taruwa ko yake wucewa da karfi yayin da ake ruwan sama.
  • Kamfanonin jiragen sama su nemi cikakken rahoton yanayi daga NiMet kafin su tsara tashi ko saukar jiragensu.

Kara karanta wannan

2027: An rugurguza allunan tallata Tinubu, 'yan APC na korafi

Karanta hasashen yanayin a nan kasa:

Hasashen rana da ruwa a Najeriya

A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto cewa NiMet ta yi hasashen cewa jihohin Arewa za su fuskanci zafi da rana tare da yiwuwar tsawa da ruwan sama.

A bisa hasashen hukumar a jihohin Arewa ta Tsakiya, ana sa ran samun ruwan sama tun da sanyin safiya sannan a samu rana daga baya.

A Kudu kuwa, NiMet ta ce za su fuskanci ruwan sama mai yawa wanda ka iya haddasa cunkoso da jinkirin zirga-zirga abubuwan hawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com