Gwamna Ya ba Tinubu Takobi, Ya Fadi Bangaren da Ya Ke Son Ya Yaka
- Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya roki alfarma daga Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
- Gwamnan ya bukaci Tinubu ya ci gaba da yaki da laifuffuka da cin hanci da kuma ta'addanci a fadin kasar baki daya
- Ya tabbatar da cikakken goyon bayan yan Ogun ga shugabancin Tinubu inda ya ce yan jiharsa suna tare da shugaban
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abeokuta, Ogun - Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, ya nuna godiya ga shugaban kasa, Bola Tinubu, bisa ziyarar da ya kai jihar domin kaddamar da manyan ayyuka.
Abiodun ya bukaci shugaban kasar da ya ci gaba da yaki da aikata laifuffuka a kasar da kuma ta'addanci da ake fama da shi.

Source: Twitter
Abiodun ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a X, inda ya ce ya mika wa shugaban kasa takobin girmamawa a matsayin wata alama ta yabo.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito kan zargin Tinubu da haddasa rikicin ADC bayan hadewar Atiku, Obi da Kwankwaso
Gwamna ya kwarara yabo ga Bola Tinubu
Ya ce ya samu damar gode wa Tinubu bisa ziyarar da ya kai Ogun domin kaddamar da filin jirgin sama na 'Gateway' da kamfanin jiragen sama na jihar.
Gwamnan ya kara da cewa an kuma kaddamar da jirgin dakon kaya na farko tare da wasu muhimman ayyuka da za su inganta tattalin arziki.
Abiodun ya bayyana cewa bai wa Tinubu takobin na da nasaba da mukaminsa na gargajiya na Jagaban, yana mai kira gare shi da ya ci gaba da yaki da laifuffuka da cin hanci.
Sanarwar ta ce:
"Na mika masa takobin girmamawa a matsayinsa na Jagaban (jagoran mayaƙa/masu cin nasara), ina ƙarfafa masa gwiwa ya ci gaba da yaƙi da laifuka da aikata laifi, da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa, musamman yayin da yake shirin sake tsayawa takarar wa’adi na biyu, tare da tabbatar masa cewa a Ogun muna goyon bayansa."
Ya kuma bukaci shugaban ya dage wajen shawo kan matsalolin kasa yayin da yake shirin sake neman zabe a karo na biyu.

Kara karanta wannan
Bayan hare haren da aka kai a jihohin Arewa, Tinubu ya tunkari matsalar tsaro gadan gadan
Gwamnan ya jaddada cewa jama’ar Ogun suna tare da Tinubu dari bisa dari wajen ci gaban kasa.

Source: Facebook
Tinubu ya kaddamar da ayyuka a Ogun
A ranar Asabar ne 4 ga watan Afrilun 2026 shugaban kasa ya ziyarci Ogun inda ya kaddamar da filin jirgin sama na 'Gateway' da kuma kamfanin jiragen sama na jihar.
An bayyana cewa wadannan ayyuka za su kara bunkasa sufuri da kasuwanci a yankin da samar da ayyukan yi ga al'ummar jihar.
Haka kuma ana sa ran shugaban zai kaddamar da karin ayyuka a fannoni daban-daban domin inganta tattalin arziki da tsaro.
Gwamna Abiodun ya nada hadimai 1,200
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Ogun ta kafa tarihi a jihar bayan nada hadiman gwamna na musamman mafi yawa a kan harkokin siyasa.
An nada mataimakan na musamman kan siyasa 1,200 domin inganta alaka da jama’a cikin mulki saboda kara kusanci da gwamnati.
Majiyoyi sun ce an yi haka domin yada ayyuka da amfanin dimokuraɗiyya a dukkan kananan hukumomin da ke jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng