Ya Haura N1,215: Ƴan Kasuwa Sun Sanar da Sabon Farashin Man Fetur a Najeriya

Ya Haura N1,215: Ƴan Kasuwa Sun Sanar da Sabon Farashin Man Fetur a Najeriya

  • Ƙungiyar manyan dillalan man fetur ta Najeriya (MEMAN) ta sanar da cewa kuɗin shigo da litar fetur ya haura N1,380 a farkon watan Afrilu
  • Farashin gangar ɗanyen mai na Brent ya kai kusan $108, yayin da Bonny Light na Najeriya ya haura $100, wanda hakan ya jawo tsadar tataccen mai
  • MEMAN ta fitar da rahoton yadda ake sayar da fetur, dizal, gas din girki, gas din CNG, man jirgi a wasu sassan Najeriya kamar Legas da Warri

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas – Ƙungiyar manyan dillalan man fetur na Najeriya (MEMAN) ta fitar da sabon rahoton da ke nuna gagarumin sauyi a farashin man fetur a sassan ƙasar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, MEMAN ta ce kuɗin shigo da litar man fetur Najeriya ya tashi daga N971 da aka gani a ƙarshen watan Maris zuwa sama da N1,380 a farkon watan Afrilu.

Kara karanta wannan

'Kowa sai ya mutu': Trump ya fadi lokacin da zai 'shafe' Iran daga doron duniya

'Yan kasuwar sun sanar da sauyin farashin fetur da gas da aka samu a Najeriya.
Wani ma'aikaci yana sayar da man fetur a gidan mai. Hoto: Benson Ibeabuchi/Bloomberg via Getty Images
Source: Getty Images

Farashin fetur daga rumbunan ajiyar mai

Wannan tsada na da alaƙa da tashin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya, inda Brent ya kai $108 sannan WTI ya kusanci $100, a cewar sanarwar da aka fitar a shafin MEMAN na X.

Sanarwar ta yi nuni da cewa dillalan mai na biyan kuɗi daban-daban na daukar mai daga rumbunan ajiya, kuma kudin na bambanta ne saboda bambancin yankin da suke ɗibar man.

A Legas, farashin ya kai N1,218.50 zuwa N1,300.00 yanzu, yayin da aka sayar da shi a kan N1,215 a ƙarshen Maris yayin da a Warri, farashin lita ɗaya yanzu ya koma N1,250.00 zuwa N1,300.00.

Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa a Calabar da Fatakwal, ana sayar da litar fetur daga N1,235.00 zuwa N1,335.00.

Farashin sauran kayayyakin mai

Baya ga fetur, sauran nau'ukan makamashi ma sun sami ƙaruwar farashi sakamakon hauhawar farashin dala da kuɗin sufuri yau:

Kara karanta wannan

Iran ta nuna wa Trump yatsa, ta lalata hatsabiban jirage da Amurka ke ji da su

  • Dizil: A Legas yana tsakanin N1,780 zuwa N1,955, yayin da a Fatakwal yake N1,350 zuwa N1,850.
  • Gas din girki: Kilogiram ɗaya yanzu yana tsakanin N845 zuwa N1,050.
  • Gas din CNG:Tsakanin N300 zuwa N500 a kan kowace lita.
  • Man jirgi: Lita ta tashi daga N1,536 zuwa N1,715.
'Yan Najeriya suna shan fetur da araha idan aka kwatanta da wasu kasashen Afrika.
Wasu mutane sun yi layi a gidan mai a kokarin sayen fetur. Hoto: Bloomberg
Source: UGC

Farashi a Najeriya da makwabtan kasar

Rahoton na MEMA, wanda aka kuma wallafa a shafinta na LinkedIn, ya nuna cewa duk da wannan tsadar, har yanzu farashin man fetur a Najeriya yana da rahusa idan aka kwatanta da wasu ƙasashen yammacin Afirka kamar Sierra Leone, Senegal, da Ghana.

Sai dai kuma, kiyasin kuɗin shigo da mai ya nuna cewa litar fetur na iya kaiwa tsakanin N1,700 zuwa N2,300 idan aka yi la'akari da dukkan kuɗaɗen fito da inshora.

Masana na ganin muddin farashin ɗanyen mai bai sauka a duniya ba, to farashin fetur a Najeriya zai ci gaba da hauhawa, duk da ana tace shi a cikin gida.

Matsayar gwamnati kan farashin fetur

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnatin tarayya ta yi ƙarin haske kan farashin fetur a Najeriya yayin da ake yaki a Gabas ta Tsakiya.

Gwamnatin ta ce ba za ta saka hannu wajen kayyade farashin fetur ba duk da tashin hankali a yankin da ya jawo sauye-sauyen farashin mai.

Ministan kudi Wale Edun ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta bullo da wasu matakai domin rage nauyin tsadar rayuwa ga ‘yan Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com